Ziyarar gwarzon Shahidinmu Ishaq Muh'd Suleman !!!


 

Ma'asumah Ng News Update

Tare da Shana islam✍️.


Tagawar Wakilan SHAFIN MA'ASUMAH NEGIRIAN NEWS UPDATE Sun Kai Ziyara a Makwancin Shahid Ishaq Muhammad Suleman, Dake garin Birin Tudu Mafara Zamfara State, Wannan Ziyarar ta Gudana ne a makon da yagabata Bayan fita daga Program din Mu'utamar da Shafin na Ma'asuma Negeria News Update ya Shirya a garin Shankafi dake cikin Jihar ta Zamfara.


Bayan Kammala taron ne Wakilan na Ma'asuma Sukayi Tawaga Zuwa garin na Birin Tudu isar su garin keda wuya ba tare da bata lokaci ba suka garzaaya zuwa wajen Mahaifin Shahidin inda sukai Masa Ta'aziya ta Addu'o i, Mahaifin Na Shahid Ishaq Muhammad Suleman ya jidadin wannan Ziyarar Sosai inda yaita Godiya dasa Al'barka ga Maziyartan daga karshe a kayi Addu'a.


Bayan Kammala Addu'a sai Tagawar Maziyartan suka Kama Haiya zuwa Makabarta domin Ganin Shahidin danyin Musharaka da juna, An dauki haiyar Makabartar tare da Paster ta Bana Mai dauke da Hotonan Shahid Ishaq Muhammad Suleman, sannan Maziyartan suna tafiya suna rera Wakokin Shuhada a ciki harda wakar Shahidi Ishaq Muhammad Suleman, Haka sukaci gaba da tafiyar har isa Makwancin'sa.


Maziyartan Sun Isa Makwancin Shahidin kowa na cikin Shauki da Muradin ganin GWARZON Shahidin domin Shakowa da Soyayyar Dake cikin zukatan Bayin Allah Isar su keda kowa kowa yazama Dan Hidima ga Shahidin inda aka sake wanke Makwancin Tas aka sake tsabtace shi Zukata na Cikin Shauki da Jimamin Rashin GWARZON Shahidin a cikin su,


Bayan Gama tsabtace Makwancin Aka Karanta Ziyara da yin Addu'o i sannan Kuma wasu daga cikin Maziyartan suka kasa hakuri su tafi saboda Shakuwa da Soyayya Haka suka Kama Ziyaran Shahidin daya bayan daya A lokaci daya ba Abunda kakeji A wajen sai sautin Kukan Bayin Allah Badan ya yi Shahada sukewa kuka ba a a saboda Mahimmancin sa a cikin su da Halayin shi na gargaru da iya zamantakewar shi da mutane' duk cikin Wakilan SHAFIN MA'ASUMAH suna son kancewa tare da Shahid Ishaq Muhammad Suleman Amma yau gashi an wayi gari ba a tare da shi sai dai Ziyara wannan Kewar ce tasa bayin Allah kuka a wajen.


Bayan Haka Dan uwa Ammar Usman Sabo yayi wasu bayanai a wajen lokacin da ake Ziyara naso ace na rike jawaban saboda Mahimmancin su ya dace ace nakawa kowa yaji Amma ayi mun Afwn saboda Gazawata tasa na kasa rikewa Amma a cikin Bayanan nasan Zan iya tuna inda yake cewa yanzu Shi Shahid Ishaq ya Huta ya Gama aikin sa mune kawai ya rage muyi namu aikiin,yake cewa Shahid nada Hakki akanmu idan Muka kasa saukewa wlh zai kalubalance mu Dan Haka ya rage namu yin abunda ya tace ga Shuhada dansu sunyi dace sun wuce wajen tasu tayi kyau.


Allah sarki Zan iya tuna lokacin da zamu wuto mubar Makwancin nike cewa Auwal m Tukur Nace Allah sarki A Kano na fara ganin Shahid gani na farko gashi gani na biyu yazama Ziyarar Makwancin'sa ne Ya Allah Amincin Allah ya tabbatar ga SHAHID ISHAQA SULEMAN tun Ranar da akai Haifeka Da Ranar da kayi Shahada har izuwa Ranar da za a tasheka kana Mazlumi.


Shana Islam Shana Islam

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post