*****************************************
A zantawar mu da Dan uwa Samaila yake cewa 'yan bindigar mutum 11 ne, da zuwansu suka fada cikin dakin sa amman basu samu damar gani na ba, sai suka ce lalle na bayyana ko su shiga cikin gidanmu su kashe kowa ko kuwa suyi yekuwar taimako mutanen gari su fito, wajen kawo agaji su bude masu wuta!
Allah sarki yace aran shi tunda shi suke nema da a kashe mutane saboda shi gwara shi a kashe shi sai ya bayyanar masu daya daga cikin su ya sara masa adda a kai take addar ta lankwashe,suka harbe shi sau 5 sai dai kawai ya kakkabe rigar sa alburushin suka zube a qas, daga bisani suka ce masa to kawai zamu tafi da kai yace to bisimillah.
Su goma sha dayan (11) suna rike da shi saboda sun san zai iya kara 6acewa yale kuwa bai 6ace ba har suka isa "Deport" din su, a nan yace masu to ya za'ayi? Magana zamu yi da ku ko kuwa? Suka ce ba wannan ba kashe shi suke so suyi! Yace to shike nan suka fara kokawa Allah ya bashi nasara da hannu ya kai mutum 6 a qasa, sauran 5 da suka fahimci ba rawa ba tumami sai suka jefa igiya a kafafunsa suka kaishi a qas! Ya Allah😔
A nan suka dinga taka shi da mashin bayan nan mutum 2 suka zo suna kokari karya wuyansa Allah bai basu iko ba sun juya kanshi amman ina Ajalin baiyi ba, daga bisani da suka fahimci ya mutu sai suka tara ciyayi suka banka masa wuta suka tafi abunsu😭 hallau dai a nan ma kayan jikin sa kawai suka kone, bayan ya farfado sai ya taso ya nufo hanyar gida dai_dai lokacin alfijir ya keto gari ya soma wayewa ya samu wuri ya zauna ta inda za'a iya ganin sa idan an biyo sawun shi.
Kadan kenan akan abunda ya faru da Dan uwa #Samaila
Alhamdulillahi yanzu yana kar6ar magani kuma sauki na shiga, muna kara baran addua ga 'yan uwa🙏
*Al'ansar*