Zazzafan Alqalaminmu a yau: Sisters sunfi cutuwa fiye da Brothers cikin zamantakewar Aure.. – Malam Ado Isah Guda



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

A fagen zamantakewar aure sistoci sunfi hakurin zama da {brothers} fiye da hakurin da brother ke yi akan sister. Wannan zance nawa gaskiya ne, domin sau nawa muke ji (brothers) na cutar (sisters) ?


Duk lokacin da zaka ji ana shari'a tsakanin sister da brother akan auren su sai kaji mafi yawa shine ke cutar da sister. Za ka fahinci hakan ne yayin da ka fara bibiyar shari'ar tasu, sai kaji zancen brother ne mugu baya kula da sister, cutar ta ya ke yi, ba ya ci yar da ita gwargwadon ikon da Allah ya ba shi, imma yana iya ciyar da ita to, ba abinci mai kyau yake bata ba. 


Ba ya kula da lafiyarta ballantana na 'ya'yan da ke gabanta, baya kawo kawo mata abin wanki don kyautata tsabtarta , balle kuma ya yi mata sabon kaya wanda za tasa taji cewa lalle fa ita ma mace ce kamar saura ba.


Wani lokaci kuma sai kaji an ce sister ce ta samu kudinta, brother ya karfe da sunan aro ya cinye ya hana ta, ko kaji an ce ai tunda ya aure ta ne bai taba mata sutura ba tun kayanta na aure bai taba mata wasu ba nata sun kare sun lalace yaki yayi mata wasu ya barta da tsummokara. Haka dai muke jin irin wadannan shari'o'i na gudana tsakaninsu.


Amma a haka ana fara magana sai kaji (brother) na cewa, " NI BA'AMIYA ZAN AURA !" To, ga sister ma wacce tafi ba'amiya hakuri da juriya bata iya zama da kai ba saboda cutar da ita da kake yi har hakurinta ya kare tabar gidan ka, ina kuma ga wata bola (Ba'amiya) wacce bata sha ruwan tarbiyya ba ?


 Haba dan'uwa, a ina ne zaka iya kula da ita ba'amiyar ga sister mai hakuri ma baka kula da ita ba ? Ka aure sister kyakkyawa tazo gidanka ta koma mummuniya tsabar wahalar da kake bata ? 


Wani abu ma wlh banda darajar (Set) da sistoci ke sawa yau da kullum da asirin su ya tonu da yawan gaske saboda rashin suturar da (brothers) ke yi musu😭.


A hakan ne brother ko kunya bai ji idan ana magana akan sistoci kaji ya bude baki da cewa, 


" HMMM, AI SISTOCI BASU MUTUNCI, GA GIRMAN KAI GARE SU DA JIJI DA KAI ! AI SISTER SAI A HANKALI ."


Haka za kaji yana fada saboda baya tsoron Allah, ya take laifinsa yana hangen nata, ga rashin tausayi daga wasunsu. Idan anje gidansa mugu ne ita ke hakuri da shi, amma a haka yake son ba'amiya da aure wacce ba asirinsa zata rufe ba sai dai ma ta tona masa😄.


'' TO, BROTHERS MASU SON AURAN BA'AMIYYA KU JE ALLAH YA RAKA TAKI GONA''.


@ Abubakar Aliyu Ahmad Ningi. 


     9th January, 2021.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post