Zantukan shaik hafiz jalaludin suyudi(RA)
Hafiz jalaludin suyudi ya rubuta wata kasida mai baitoci ashirin da bakwai wadda ke da suna Tuhfatul muhtadina Bi'akhabaril mujaddadina, wadda kuma a cikinta ya yi bayani akan hadisin annabi mai tsarki (SAW) Wanda ke magana kan tayar da mujaddadin musulunci bayan kowane karni ya kuma kawo sharudda guda tara wadanda da su ne ake gane kowane majddadi.
A takaice, ba muna nufin mu kawo dukkanin abin da kasidar ta shehin malamin ta kunsa bane. Ba kuma muna nufin mu kawo dukkan fassarar kasidar tasa a nan bane. Sai dai kawai za mu kawo fassarar wadansu baitoci wadanda ke da nasaba da janibobin da muke magana akai watau zancen bayanin hadisin tayar da mujaddadi da kuma sharuddan gane mujaddadi.
Bayan shehi malamin yayai godiya ga allah(SWT) a baitin farko na kasidar, ya kuma gabatar da salati ga manzon Rahama(SAW). A baiti na biyu, sai kuma yaci gaba da jero baitoci uku wadanda a cikinsu ne ya yi bayanin hadisin tayar da mujaddadi. Ha yadda ya kawo baitocin:
Hakika ya riga ya zo a hadisi mashahuri,
Wanda dukkan malamin hadisi mai lura ya rawaito.
Baiwa a gare ta, da malamin da ke jaddadawar,
Addinin shiriya dimin shi mujtahidi ne.
A kuma inda ya yi zancen sharuddan gane mujaddadi ya kawo baitoci biyar ne, kamar haka: shardin kuww a wannan, shekaru dari su shude,Alhali shi yana rayea tsakanin mutane.
Yana shiryarwa da ilimi izuwa ga matsayinsa, yana kuma tainakon sunna a zantukansa.
Ya kuma kasance ya jada dukkanin fanni, kuma iliminsa ya kewaye ma'abota zamaninsa,ya kuma kasance a cikin hadisi ya ruwaito ne, Daga iyyalan gidan al-mustapha,kuma an karfafa. Kansantuwarsa mutum daya kuma shine mashahiri,haka ne hadisi da ijma'in malamai suka fada.
Wadannnan a takaice sune baitocin da imama suyudi(RA) YA gabatar a kasidara yanabanin hadisin mujaddadi da matsayin mujaddadi na ilimi da kuma sharuddan gane mujaddadi.
Zantukan majaddadi shehu usman dan fodiyo(TR)mujadda.