@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
Misali ne ace matar ka tayi maka abinci ta kawo ma domin kaci, bayan ka fara ci sai kaji barkono ya yi yawa a cikinsa kai kuma ba ka son abinci mai barkono, to, abu ne mai kyau kayi mata magana a cikin hikima wacce zaka yi ka sanar da ita domin ta gyara. Mai makon a lokaci guda ka bude baki kace mata barkono yayi yawa a abincin nan .
'Dan'uwa idan kayi haka din matar ka baza taji dadi ba gaskiya, don ka kushe kokarinta ne da tayi akan ka. Yana da kyau a gare ka dan'uwa ka nuna farin cikinka akan iyawarta kawai ka yabi abincinta sosai ka nuna mata abincin ya yi dadi ya yi (Normal) yanda kake so, kuma za kayi haka din ne cikin zancen hikima, zaka faranta ran matar ka kuma zai ta ji dadi sosai a lokacin da kake yabon iyawarta. Wallahi bayan ka gama haka din zaka iya cewa kowai ya yi dedai. Ranki ya dade Uwar gida Na so ace ma barkono nan be kai haka yawa ba da sai yafi dadi sosai don kinsan Ni ina 'Ulcer' ne idan kika din rage yawansa din a abincin na zai fi dadi. Kayi mata haka din a cikin murmushi da sakin fuska , Insha Allahu gobe sai kaga ta gyara fiye da na yau din da ka ci.
Lallai haka ne 'yan uwa duk wanda ya yi kuskure yana bukatar a gyara masa amma idan za aje ga gyaran nasa din ana bukatar a fara nuna kokarinsa mai kuskuren din, domin yaji dadi idan aka yi masa haka zaiji gwarin gwaiwa sosai wajen gyarawa bayan haka din sai aje ga kurkurensa cikin sayin murya ayi masa maganar hikima wacce zai gamsu da ita ba tare da an kushe masa gazawarsa ba.
'A daure a koyi zancen hikima wajen gyara kuskuren mutum, domin iya maganarka ce kesa mutum ya fahimcen ka a lokacin da yake maganarka. A dena nuna gazawar mutum a lokaci guda haka din bai dace ba.
Yaa Allah ka kara mana jagoranci acikin al'amuran mu duk wani kuskuren mu Allah ka bamu ikon gyarawa.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏼Abubakar Aliyu Ahmad Ningi.
07/01/2021.
Tags:
Tunatarwa