@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
IDAN BA KA YARDA DA ABUBUWA UKUN NAN BA KA RIQI WANI UBANGIJI KAWAI WANDA BA ALLAH BA
Ya zo cikin hadisil-Qudsiy wanda Manzon Allah (S. A. W. W) ke riwaitowa daga gare Shi yana cewa,
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
Allah (T) na cewa
" DUK WANDA BAI YARDA DA HUKUNCINA (qaddara) BA , KUMA BAI GODE GAME DA NI'IMOMINA BA, KUMA BAI YI HAQURI AKAN BALA'I NA (jarrabawa) BA, TO, YA RIQI WANI UBANGIJI (a matsayin Ubangijinsa) KOMA BAYAN NI ."
وَ قَالَ النَّبِيُّ ص يَقُولُ اللَّهُ عَزَّ وَ جَلَّ مَنْ لَمْ يَرْضَ بِقَضَائِي وَ لَمْ يَشْكُرْ لِنَعْمَائِي وَ لَمْ يَصْبِرْ عَلَى بَلَائِي فَلْيَتَّخِذْ رَبّاً سِوَائِي[38].
Saboda haka yana daga cikin imani yarda da qaddara da godiya bisa n'imomin da Allah yayi, da kuma yin haquri cikin dukkan wata jarrabawa da mutum ya sami kansa ciki.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.
(08137925034)
6th January, 2021/ 23rd Jimada-Ulah, 1442.