Shafin sada zumunta na twitter, ya sanar da dakatar da shafuka 70,000 dake da alaka da gungun magoya shugaba mai barin gado na Amurka, Donald Trump.
ABNA24 : Twitter, ya ce ya dakatar da shafukan ne domin kaucewa yin amfani dasu domin tayar da irin boren da ya faru a makon da ya gabata a birnin Washington.
An dai fara toshe shafukan ne tun bayan da aka dakatar da shafin shugaban kasar ta Amurka Donald Trump, bayan da magoya bayansa suka suka kutsa a cikin ginin majalisar dokokin kasar da nufin hana muhawarar da ake ta tabbatar da nasarar Joe Biden a hukumance a matsayin zababben shugaban kasar.
Wata sanarwa da shafin twitter, ya fitar ta ce shafukan na yada bayanai masu hadari, a daidai lokacin da ake tunkarar bikin rantsar da zababen shugaban kasar Joe Biden a ranar 20 ga watan nan.
Rahotanni daga AMurkar na cewa akwai yiwuwar magoya bayan Trump, su tayar da hargitsi gabanin bikin.
Kutsen da magoya bayan Trump, sukayi a ranar Laraba data gabata, a majalisar dokokin kasar ya dai zubar da kimar Amurka a idon duniya.