ADALCI SHINE YAKE WANZAR DA ZAMAN LAFIYA.
Tsakanin Masu Zan-Zangar Kubutar Jarumin Matashi Samaila Isah Laga, da 'Yan Ta'adda (MAHARA), Da suka Shigo har cikin gari Cikin gidan su Sukayi Garkuwa dashi Wanene Ya kamata Doka tayi Aiki akan shi?
Idan Adalci Za'ayi Tunda Har Ansan Shugabanin 'Yan Ta'addan da Suka Shigo Har cikin gari Sukayi Garkuwa da Wannan Matashi Wanda Sanadiyyar Faruwar Hakan ne Ya Fusata Matasa Yin Zanga-Zanga Lura da Sanin Muhimmancinsa ga Al'umma da Kuma tunanin da Al'umma Sukeyi na Yanayin da Gari Zai kasance Idan Aka kawar Masu da Wannan Fasihi Kuma Zakakurin Matashi.
Eh, Lalle Anyi Zanga-Zanga Kuma Bana goyon Bayan 6arnata Dukiyoyi da Kai Hare-Hare Wurare daban daban da Matasan Sukayi Amma lalle Dole Sai Anyi Adalci tsakanin Matasa Masu Zanga-Zanga da Barayi Masu Kokarin Kashe Wannan Matashi.
Ko ba komai Tasirin Abinda Matasan Sukayi Ya Kubutar da Rayuwar Wannan Jarumin Matashin daga Salwanta, Domin Zan-Zangar itace ta Nuna Hakikanin Muhimmancin Wannan Bawan Allah ga Al'ummar gari Kuma Hakan da Al'ummar Gari Sukayi Shine Ya Nuna Hatsarin da Suke kallo garinsu Zai Shiga Idan Aka Salwantar da Rayuwarsa ta Hanyar Yi masa kisan gilla.
Idan Gwamnatin Jahar Zamfara na Neman Samun Dawamammen Zaman lafiya Dole Sai ta kasance Mai yin Adalci a tsakanin Al'ummar ta Batare Nuna Fifiko a tsakanin Al'ummar ta.