Ibrahim Daurawa.
Tashin hankali da ya faru ranar 7/01/21, a Majalisar Dokokin Kasar Amurka ya sake bayyana irin shingen da yake tsakanin al'ummar Kasar Amurka.
Akasarin Magoya bayan Donald Trump fararen fatar Amurka ne wadanda suke ganin Trump a matsayin wani jan Gwarzo da zai daukaka Fararen Fatar Amurka da kasar Amurka. Don haka suka amince da shi a wanda yake Wakilta tunaninsu da dukkan ra'ayinsu na buwayar Fararen Fata abirbishin bakaken fata da sauran Jinnsin da ba farar Fata bane Zalla.
Duk Karerayin da Rashin Mutunci da keta dokar da Tsarin Mulkin Amurka da Trump ya kwashe Shekara hudu yana yi, ba su dauke shi a bakin komai ba.
Wannan ya bashi damar mike Kafa da ci gaba da daukan kasa kamar wani gunkin Amurkawa Fararen Fata.
Shan kayen da ya yi a watan November, ya tayar da ciwon haukan da yake damunsa. Wanda Masana cutar Kwakwalwa da halayyar dan Adam suka dade da Sanarwa cewa Trump yana da tabin Kwakwalwa. Bayan haka Yar uwars ma ta sanar da Duniya hatsarin tabin Hankalin da yake damunsa.
Tun kafin a kammala kidaya Kuru'un da aka kada ya ce an yi Magudi sai an sake zabe, ya dawo ya ce dole a yi watsi da Kuru'un wasu mahimman Jihohi. A karshe dai ya ce an tabka Magudi a fadin Kasar. Wani lokacin ya ce an sace Injinan kirga Kuri'a ko baddaala su. Dole ta saka aka sake kirga Kuru'un wasu Jahohin masali an Jahar Georgia an sake Kirgawa har sau Uku. Amma duk da haka a ranar 2/01/21 aka nadi Muryarsa yana baiwa Sakataren Jahar Georgia umarni ya nemo masa Kuru'u 11780. wanda za su bashi Nasara sauya Zaben da ya sha kasa.
Rudi Juliani babban Lauyan Trump ya shigar da kara Kotunan Amurka daban daban har zuwa Kuton kuli amma ya kasa kawo Shaidar an yi Magudi, abin da ya sa aka yi watsi da Kasarsu.
Abu na karshe da Trump ya yi shi ne ya kirawo Gangami ya harzuka magoya bayansa ya ce su mamaye ginin Majalisar Kasar Amurka, ranar da za a kirga Kuru'un masu tabbatar da zaben Shugaban Kasa wanda da su komai ya kammala sai rantsar da shugaba a ranar 20 ga January.
Tashin hankalin da ya faru a wannan rana ya fito da irin shirin da Trump ya yi na amfani da tashin hankali da tsoratarwa don a tilastawa masu jefa Kuru'un jefa masa abin da zai bashi damar yin Juyin Mulki ta amfani da Kuru'a ko a hana kirga Kuru'un, abin da zai bashi damar kafa dokar ta baci ya saka Sojoji sake shirya sabon Zabe ya yi tuwo na mai na.
Magoya bayan Trump sun amsa kiransa sun shigo Birnin Washington daga Jahohi daban daban na Amurka da shirin kwace Zabensu da suka ce an kwace musu ta hanayar Magudi.
Jami'an tsaron Gine-ginen Majalisar Amurka da Hukumomin tsaron Amurka, ba su dauki matakin hana su shiga ba. Wasu ma na cewa sun bude musu hanya ne, na ga wani Video clip wani Jami'in tsaro yana kiran masu Zanga zangar su taho zuwa cikin Majalisar.
Sun haura shingayen, wasu ta katanga wasu ta fasa Tagogin suka shiga, suka kuma dirfafi yan Majalisar har sai da suka arce zuwa maboya a karkashin Kasa.
Mutane hudu ne suka Mutu a wasu suka Jikkita a samakon wannan tarzomar da Trump ya kira. An tarwatsa Ofisoshi da watsi da takardu. Yan Daba sun hau Kujaera Shugaban Majalisar Dattijai sun yi iskancinsu. Sun kwashe tsahon Awa Uku babu wanda ya hana su duk abin da suke so. Ba aka kawo daukin Jami'an tsaro haka suka ci karensu ba Babbaka.
Amma lokacin da aka yi Zanga zangar black lives matters, bayan Kisan George Floyd. An kawo Yan Sandar Birnin Washingon dana wasu Jahohin, da dubban Jami'an tsaro na National Guard, ga kuma FBI a cikin shirin Yaki wasu a Mota wasu a Kekuna wasu a Kasa wasu da Uniform wasu da fararen Kaya tun kafin Masu Zanga Zangar su taro, sun Kewaye Gine-gine da Kadarorin Gwamnati.
Donald Trump ya nemi a kawo Sojojin Kundumbalar na Amurka su farwa masu Zanga zangar. Shugabannin Majalisa da Mayo na Washington ne da wasu tsaffin Janarorin Sojan Amurka sun taka masa burki.
Amma a wannan Mayo din Washinton tun kafin masu Zanga Zangar su taru ya nemi a kawo Naitonal Guard da yan Sanda Birnin aka hana shi. Sai yan Sanda kalilan cikin kayan Traffic babu kayan kare kai ko Makamai aka kawo suna bada hannu.
An harba Harsashin Roka da ruwan tear gas akan Mutane har da Yan Jarida an doki wasu haka siddan, An watsa ruwan zafi akan Mutane an kuma fasa Kayan aikin Yan Jarida a lokacin BLM.
Amma a wannan karon duk babu daya da ya faru, Sai Yan Sanda ne suka daukan Selfie da Masu Tarzomar. Saboda suna ganin su a Matsayin Fararen Fata da suke kare Muradin na Kafa Trump a Kujerar Mulki ko ta halin Kaka.
Mutane sama da dari biyar aka kama a zanga Zangar BLM a rana daya, aka hana mutane Zirga-Zirga, amma a wannan mutane 47 kacal aka kama, yawanci kuma an sallamesu. Duk wadanda suka yi fashe fashen nan sun koma gida lami lafiya. Suna fada suna cewa suna alfahari da abin da suka yi. Jami'an tsaro na kallonsu ba su yi musu komai ba.
Bayan abubuwa sun kazance Trump ya yi magana a TV ya godewa masu Tarzomar ya kira su da sunan masu Kishin Kasa, wadanda suke kare Yancinsu. Amma a lokacin Zanga Zangar Kisan George Floyd ya kirasu da yan ta'adda marasa kishin Kasa, masu Kiyayya Zaman lafiya.
Wannan abin da ya faru ya nuna a fili cewa akwai yan Lele da kuma yan Bora a Kasar Amurka a gwamnatance. Babu wanda ya zaci abin da ya faru a Ginin Majalisar Kasar Amurka zai faru. Amma ya dai faru, kisan kai, fashe fashe doke doke da barnata Kayan Gwamnati a gaban Jami'an Tsaro. Wadanda suka aikata sun gama sun tafi lami lafiya suna alfahari da abin da suka yi. Wasu kuma Amurkawan tsaya kawai suka yi a filin aka bi su da harbi da duka da tear gas, Kisa da dauri ya biyo baya.
Wannan kuma ba komai yake nunawa sai cewa Dimokaradiyya Amurka kayar ce da Munafunci. Ba kuma zata zama mafita ga matsalolin Kasar ba, har ta fitar da wasu Kasashen.
Wani abu da wannan yake nunawa shi ne karshen Daular Amurka ya karato. Daulolin da aka yi a Tarihin Duniya suma daga ciki suka rushe ba daga Waje aka kawo musu hari aka rusa su ba, Duk lokacin da masu Mulki suka kasa tabbatar da adalci a tsakanin Talakawansu har suka rabu gida-gida kowa na kallon kowa a matsayin abokin gaba, wannan Gwamnatin Karshenta ya gabato ba. Tabbas karshen Amurka ya zo a lokaci kawai ake jira ta watse.. Wannan farko ne tsarin ya dade da rubewa yanzu ne cutar ta fara bayyana a fili. Yanzu dai an fara daga Tutar Confederate.