Sirrin neman soyayya daga mutane !!!


 

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


IDAN KA SAMI SOYAYYA DAGA MUTANE ZA KA SAMI TA ALLAH 


Babban ma'auni na gane matsayin mutum wajen Allah shine yadda mutanen kirki ke nuna soyayyarsu gare shi. Kun san akwai mutumin banza wanda ke samun soyayya daga mutane, sai dai kuma in ka bibiya za kaga masoyan nasa ba mutanen kirki bane, (abin misali daga masoyan Buhari) . 


Allah ba zai taba sanya soyayyar mutumin banza cikin zukatan mutanen kirki ba, haka zalika soyayyar mutumin kirki ba ta shiga zukatan mutanen banza, (dau darasi daga maqiyan Sayyid Zakzaky (H) ).


Ya zo daga Muhammad Al-adda'i, daga Ash'ariyu, daga Sahal daga Ibrahim Bn Dawuda Al-Yaqubiy , daga dan'uwansa Sulaiman , da isnadi wanda aka daukaka shi, wani mutum ya cewa Annabi (S. A. W. W), 


" YAA Ma'aikin Allah (S. A. W. W) , ka sanar dani wani aiki wanda idan na aikata shi Allah zai so ni daga sama, kuma mutane su so ni daga qasa ."



Sai yace masa, 

,

 عَنْ مُحَمَّدٍ الْعَطَّارِ عَنِ الْأَشْعَرِيِّ عَنْ سَهْلٍ عَنْ إِبْرَاهِيمَ بْنِ دَاوُدَ الْيَعْقُوبِيِّ عَنْ أَخِيهِ سُلَيْمَانَ بِإِسْنَادِهِ رَفَعَهُ‏ قَالَ رَجُلٌ لِلنَّبِيِّ ص يَا رَسُولَ اللَّهِ عَلِّمْنِي شَيْئاً إِذَا أَنَا فَعَلْتُهُ أَحَبَّنِيَ اللَّهُ مِنَ السَّمَاءِ وَ أَحَبَّنِيَ النَّاسُ مِنَ الْأَرْضِ فَقَالَ لَهُ 


" KA KWADAITU CIKIN ABINDA KE WAJEN ALLAH MAI GIRMA DA 'DAUKAKA ALLAH ZAI SO KA, KUMA KA NISANCI ABINDA KE HANNUN MUTANE, MUTANE ZA SU SO KA ."


ارْغَبْ فِيمَا عِنْدَ اللَّهِ عَزَّ وَ جَلَّ يُحِبَّكَ اللَّهُ وَ ازْهَدْ فِيمَا عِنْدَ النَّاسِ يُحِبَّكَ النَّاسُ‏[15].


(2) أمالي الصدوق ص 293.


Saboda haka idan kana so Allah ya so ka, to, ka kwadaitu da son rahmomin dake Hannunsa (T) ta hanyar yi mar biyayya. Sannan in kana son mutane su so ka, to, ka rufe idanuwan daga hangen abinda ke hannunsu. Idan ka aikata haka za ka sami soyuwa wajen Allah da kuma wajen mutane. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏼Ado Isah Guda. 


         (08137925034)


6th January, 2021/ 23rd Jimada-Ulah, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post