Za’a Saki Litattafai 9 Da Aka Rubuta Akan Hajj Qassem Soleimani
- Najeeb Maigatari.
(Kwafowa da fassarawa daga jaridar Tehran Times).
Yayin da ake tunawa da shekara guda na zagayowar Shahadar kwamandodin Musulunci Hajj Qassem Soleimani da Hajj Mahdi Al Muhandis, wasu fitattun marubuta a kasar Iran sun samar da litattafai har guda 9 wadanda suka tabo wasu janibobi na rayuwar Hajj Qassem Soleimani.
Litattafan, kamar yanda jaridar turanci na ‘Tehran Times’ ta jiya ta wallafa, yau ne ranar farko da za’a fara fito da su a matsayin girmamawa ga Hajj Qassem sakamakon irin gudunmawar da ya bayar ga addinin Musulunci.
Fito da litattafan na daya daga cikin rige-rige da ake yi tsakanin kowane sashe na kasar Iran don ganin sun karrama wannan bawan Allah mai girma. Ga sunayen su a kasa:
1. I am Qassem Soleimani (Ni ne Kasim Soleiman): Littafi ne da ya kunshi tarihin rayuwar Hajj Qassem, wanda aka rubuta shi musamman domin yara qanana masu tasowa.
- Marubucin Littafi: Mohammad Hossein- Khani.
2. Uncle Qassem Soleimani (Kawu Kasim Soleiman): Wannan littafi na qunshe da labarai guda 20 ashirin wanda zasu ba yara damar yin tunani mai zurfi dangane da halayya da dabi’ar Hajj Kasim, domin daukar darasi daga gare shi, a matsayin abun koyi ga rayuwar su.
- Marubucin Littafi: Mohammad Ali Jaberi.
3. No End To This Man (Babu Karshen Wannan Mutumin): Littafi ne da yake qunshe da bayani akan yaqin da Hajj Kassem ya jagoranta domin kawo karshen qungiyar ta’addanci ta ISIS, da kuma bayani akan mahangar [Hajj Kassem] akan rayuwa da kuma fagen daga (gwagwarmaya). Har wala yau, littafin na dauke da wasu hotunan Hajj Kassem wadanda al’umma basu taba gani ba.
- Marubucin littafi: Sayyed Ali Bani-Lohi
4. Dear Soleimani(Masoyi Soleimani): Littafi ne da ya kawo tarihin rayuwar Hajj Kasim tun daga garin su Karmen har zuwa ziyarar shi Kremlin; da kuma yaqin da ya jagoranta na ruguza sojojin kasar Amerika a garin Najaf mai tsarki, har zuwa yanda ya jagoranci kawo karshen kawanya da ‘yan ta’addan ISIS suka yiwa garin Amerli a Iraqi.
- Marubuci: Hemaseye Yaran
5. A Love Story (Labarin Soyayya): Littafi ne da ya qunshi wasiyar Hajj Kasim Soleimani.
- Marubucin Littafi: Mohammad Ali Tavallai
6. Malik Of The Time (Malik din Zamani): Littafi ne da ya qunshi labarai guda 50 wadanda suka kawo kamanceceniya tsakanin Hajj Kasim da kuma Malik Al-Ashtar, sahabin Imam Ali (AS); wanda ya jagoranci yaqoqi da dama a lokacin Imam (AS).
- Marubuta: Hadakar wasu marubuta ne a kasar Iran, daga cikin su akwai Ibrahim Hadi.
7. Born In March (Haihuwar Watan Maris): Littafi ne da ke dauke da tattaunawa da abokan muqawamar Hajj Kasim akan rayuwar shi. A cikin sun kawo labarin yanda suka yi aiki tare da shi a fagen daga a lokacin fatattakar ‘yan ta’addar ISIS a kasar Syria da Iraqi.
- Marubucin Littafi: Ali Akbar Mozdabadi
8. Avertin (Sunan gari a Iran): Littafi ne da ke kunshe da bayanin wani gagarumin ‘operation’ da Hajj Kasim ya jagoranci rundunar dakarun Quds (Quds Force) a wajejen shekarar 2000 a garin Avertin da ke yankin Kerman, domin kawo karshen yan tawaye da kuma masu safarar miyagun kwayoyi.
- Marubucin Littafi: Setaragane Derakshan
9. Characteristics Of The School Of Martyr Soleimani (Dabi’un Makarantar Shahid Soleimani): Littafi ne da ya qunshi kyawawan dabi’un Shahid Kasim Soleimani ta hanyar zantukan shi da kuma labarai akan shi, domin dora duk mai son yin rayuwa irin ta shi akan hanya.
Zuwa yanzu litattafan an rubuta su da yaren Farsi ne kawai. Amma nan gaba za’a fassara su zuwa sauran yarurruka domin amfanar wadanda ba su jin yaren Farsi.
Allah Ya daukaka darajar wadannan Shahidai masu girma. Allah Ya sakawa wadanda suke kokarin raya ambaton su.