Sakon Shahid Qaseem Suleimaniy ga manyan malamai da (Maraji`ai) da masu fada aji......

_______________________________________






Takaitaccen rubutu daga sojanda yayi shekara arba'in (40) afilin daga, zuwaga manyan malamai masu girma, dakuma manyan masu fada aji wadanda suke wayarda kan al'umma.

Sojanku yahango cewa wannan tsarin da jamhuriyyar musulumci take akai, idan yalalace toh addinin musulumci daduk wata kimar dakukeda ita dakuma aiyukan dakukayi zasuzama sun lalace.

Wadannan lokutan sunada banbanci da sauran lokuta, idan har makiya sukayi nasara awannan lokacin to babu wani abu dazaiyi saura a musulumci.

Mafificiyar hanyar daza'asamu mafita kuma itace karfafa gwagwarmayar kawo sauyi, tahanyar taimakon shugaban gwagwarmaya Sayyid Ali Alkhamne'i D.Z dakuma jamhuriyyar musulumci ta Iran.

Idan kukakiyin hakan, wasu zasurika yimaku kallon masu zagon kasa a addini. Don haka kubi Imam Khamne'i D.Z sannan kutaimaka masa tahanyar wayarmada sauran mutane kai wajen yin biyayya agareshi.

Gaskiya abayyane take cewa, tsarinda jamhuriyyar musulumci take akai na shari'ar musulumci marigayi Imam Khomeini (Allah yayimashi rahama) shine ya assasa, don haka wannan tsarin yana bukatar hakikanin goyan baya da taimako.

Naga Imam Khamne'i D.Z yana fafutukar fada da zalumci shikadai, yanada bukatuwa zuwaga taimakonku da goyan bayanku, dakuma mutanen dasuke a karkashinku.

Don haka kufadakarda mutane tahanyar bayanai da zamame.

Inamai sunbatar hannunku sannan inamai neman afuwa akan abubuwan dana fada, naso yazama na'isar maku da sakonne dakaina (gaba-da-gaba) amma hakan baiyiwuba.

Sojanku kuma abokinku.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post