@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
Kafin nan ya kamata ace matashin gwagwarmaya ya kara sanin mecece waqi'a tun kafin ta same shi, domin naga yawancin matasan gwagawarmaya basu cika gane a cikin waqi'a suke ba har sai sunji harbi a jikinsu a gun muzahara ne sannan suke gane cewa waqi'a ta faru da su.
To, lallai ba iya ita kadai ce mummuniyar waqi'ar da ke samun ku ba, hatta tabarbarewar tarbiya ga rayuwarka ma waqi'a ce mai muni, idan muka nazarci al'amari za muga lalle matashin gwagwarmaya ne kashin bayan ita wannan harka din. To, a rayuwar da muke gudanarwa ta wannan zamani dabi'ar matashin gwagwamaya din ta fada cikin waqi'a yanzu, domin dabi'arsa mai kyau ce ke fita a zuciyarsa, wanda hakan ma waqi'a ce mai zaman kanta wacce idan bai yi da gaske ba za tafi wacce ta riske shi akan kwalta muni.
Matashin gwagwarmaya ne yanzu yake mummuniyar rayuwar tare da amawa cikin su ma shine uban daban majalissar su ta 'yan iska, maimakon ya zama abin koyi a gare su wajen inganta rayuwa, amma shine yake jagorantar su wajen bata rayuwa.
Matashin gwagwarmaya ne ada rayuwarsa take abar sha'awa haka zaka gan shi bai damu da al'amarin rayuwar duniya ba, burinsa a kullum harka taci gaba tare da gudummuwar sa walau ta dukiyarsa ko ta jikinsa, amma yanzu fa matashin gwagwarmaya ne zaka gano shi a gun 'yan harkokin duniya.
Inma ka ganshi acikin 'yan shaye shaye, ko masu mutuwar zuciya sata, ko masu yawon bariki ne da kuma masu neman 'yan matan banza, wasu matasan gwagwarmaya irin rayuwar da suka dauko kenan.
Ya Allah ka tausoya mana ka duba matasan mu masu irin wannan rayuwa ka basu ikon gyarata.
~Abubakar Aliyu Ahmad Ningi.
11th, January, year 2021.