@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
ZABIN ABUBUWA UKU NA GARI
Wata rana Imam Ali (A. A) yace: Yaa Ma'aikin Allah (S. A. W. W) ! Mene ne zabi na gari ?
Annabi (S. A. W. W) yace: " Zabi uku a rayuwa:
1- Zabin Abokan shawara.
2- Zabin gurin zama na kirki.
3- Zabin cin halak.
Annabi (S. A. W. W) ) ya qara masa da cewa,
" Ka zabawa 'ya'yanka abu gudu uku;
1- Zabi akan ilimi.
2- Zabin tarbiya ta gari.
3- Ka musu jagaba wajen nema masu mata na gari, in mata ne ka musu jagaba wajen taya su neman miji na gari.
KA RIQE ABU GUDA UKU
1- Zumunci
2- Adalci
3- Bari daga ha'inci
Ya Allah kasa mu dace Bi hakki A'immatu Ahlulbaiti (A. S)👏.
~Abubakar Aliyu Ahmad Ningi.
10th, January, 2021.