@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
RABUWAR KANKU RUSA GININ DA SAYYID ZAKZAKY (H) YAYI NE
Duk wanda ya nazarci da'awar Sayyid Zakzaky (H) sannan ya aunata da da'awar Manzon Allah (S. A. W. W) sai ga babu maraba ko da daidai da qwayar zarra ne. Da'awa ce wacce ta daidaita dukkan wasu qabilu mabambanta da suka amsa wannan kira.
Da'awa ce wacce ke daidaita mai kudi ko sarauta da talaka yadda babu wanda yafi wani in ba ta fuskacin taqawa ba . Wannan kuwa shine haqiqanin samfurin da'awar Manzon Allah (S. A. W. W).
A baya kafin wannan lokaci duk inda mabiyin Sayyid Zakzaky (H) yaga wani mai amsa sunan shi ma almajirin Sayyid ne, to, yakan dauke shi tamkar dan'uwansa ne na jini, kuma yakan fifita shi ma a kansa domin shi dan'uwa ne na addini wanda yafi 'yan'uwantaka ta jini.
Sakamakon jarrabawar da Allah ya jarrabi wannan da'awa da mabiyanta kamar dai yadda Allah yayi alqawarin jarraba wadanda suka riqa addini da gaskiya (firmly), sai yanayi ya haifar yadda mabiyi zai hadu da mabiyi amma maimakon ya nuna mana 'yan'uwantaka kamar yadda jagora ya koyar damu sai kaga qoqarinsa kawai shine yasan wannan dan'uwa a wanne bangare yake ciki daga mabiyan jagora (H).
An mayar da wannan harka (da'awa) ta zama bangaranci yadda kowa da inda ya juya akalarsa, kuma wai hakan da'awar Sayyid (H) ake yiwa aiki. Idan kuwa ya zama haka, to, kwatakwata an kaucewa koyarwar jagora (H).
Haqqin da ya hau kanmu shine hada kan juna da yiwa kanmu uzuri tare da yin komai namu domin Allah.
Allah (T) ya gargade mu cikin Qur'ani kamar haka :
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ ٱتَّقُواْ ٱللَّهَ حَقَّ تُقَاتِهِۦ وَلَا تَمُوتُنَّ إِلَّا وَأَنتُم مُّسۡلِمُونَ ٢٠١
" YAA KU WADANDA SU KAYI IMANI ! KUJI TSORON ALLAH BISA HAQQIN TSORONSA, KUMA KADA KU MUTU FACE KUNA MUSULMI .
A yanzu tunda dama muna cikin muslimcin, to, sai dai mu nemi yardar Allah cikin tabbatuwa kan wilayar Ahlul-Bait (A. S). Ya qara da cewa,
وَٱعۡتَصِمُواْ بِحَبۡلِ ٱللَّهِ جَمِيعٗا وَلَا تَفَرَّقُواْۚ وَٱذۡكُرُواْ نِعۡمَتَ ٱللَّهِ عَلَيۡكُمۡ إِذۡ كُنتُمۡ أَعۡدَآءٗ فَأَلَّفَ بَيۡنَ قُلُوبِكُمۡ فَأَصۡبَحۡتُم بِنِعۡمَتِهِۦٓ إِخۡوَٰنٗا وَكُنتُمۡ عَلَىٰ شَفَا حُفۡرَةٖ مِّنَ ٱلنَّارِ فَأَنقَذَكُم مِّنۡهَاۗ كَذَٰلِكَ يُبَيِّنُ ٱللَّهُ لَكُمۡ ءَايَٰتِهِۦ لَعَلَّكُمۡ تَهۡتَدُونَ ٣٠١
" KUMA KUYI RIQO DA IGIYAR ALLAH GABA 'DAYA KADA KU RARRABA (don ganin jagora ba ya tare daku (mubasharatan)). KUMA KU TUNA NI'IMAR ALLAH A KANKU (da kuma sami kanku cikin masu wilaya ga Iyalan gidan Annabi (S. A. W. W) YAYIN DA ADA KUKA KASANCE MAQIYA JUNA (sakamakon rashin samun tarbiyya irin ta iyalan Annabi (S. A. W. W) mai daidaita kowa abu guda) SAI YA CIKA TSAKANIN ZUKATANKU (da son juna) KUKA WAYI GARI DA NI'IMARSA KUNA 'YAN'UWA (na addini wanda yafi 'yan'uwa na jini), KUMA (da) KUN KASANCE A GABA NA WUTA (masu riqo da wadanda suka yiwa iyalan Annabi cin zarafi da qwacen haqqi) SAI MUKA TSERATAR DAKU DAGA GARE SHI (ta hanyar fahintar da'awar Sayyid mai nuna mana haqiqanin wadanda Annabi (S. A. W. W) ya wajabta masa yin koyi dasu). TO, KAMAR HAKANE ALLAH KE BAYYANA MUKU AYOYINSA KO ZA KU SHIRYU (ta hanyar ganin wannan jarraba da kuke ciki) .
وَلۡتَكُن مِّنكُمۡ أُمَّةٞ يَدۡعُونَ إِلَى ٱلۡخَيۡرِ وَيَأۡمُرُونَ بِٱلۡمَعۡرُوفِ وَيَنۡهَوۡنَ عَنِ ٱلۡمُنكَرِۚ وَأُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡمُفۡلِحُونَ ٤٠١
" KUMA (a sami) WATA AL'UMMA DAGA CIKINKU TA KASANCE TANA YIN KIRA ZUWA GA ALKHAIRI (na haduwar kawunanmu) KUMA TA RIQA UMARNI DA KYAKKYAWA (qaunar juna) KUMA MASU HANI GAME DA ABIN QI (kaucewa dukkan abinda zai iya kawo rarraba), TO, WADANNAN SUNE MASU RABAUTA .
وَلَا تَكُونُواْ كَٱلَّذِينَ تَفَرَّقُواْ وَٱخۡتَلَفُواْ مِنۢ بَعۡدِ مَا جَآءَهُمُ ٱلۡبَيِّنَٰتُۚ وَأُوْلَٰٓئِكَ لَهُمۡ عَذَابٌ عَظِيمٞ ٥٠١
" KUMA KADA KU KASANCE KAMAR WADANDA SUKA RARRABU (gida-gida) KUMA SUKA SASSABA (a ra'ayoyinsu na bin son zuciya) DAGA BAYAN HUJJOJI BAYYANANNU SUN ZO MUSU (daga jagora) , TO, WADANNAN GARE SU AKWAI AZABA MAI GIRMA !"
(AL-IMRAAN:102-104)
Wasu daga cikinmu kuwa qiyayyar wasu ce kawai ta dame su har ta kaisu ga fakewa dasu suna yiwa da'awar Sayyid (H) saddu. Saboda haka Allah (H) ke qara gargadinmu da cewa,
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
.........وَلَا يَجۡرِمَنَّكُمۡ شَنَـَٔانُ قَوۡمٍ أَن صَدُّوكُمۡ عَنِ ٱلۡمَسۡجِدِ ٱلۡحَرَامِ أَن تَعۡتَدُواْۘ وَتَعَاوَنُواْ عَلَى ٱلۡبِرِّ وَٱلتَّقۡوَىٰۖ وَلَا تَعَاوَنُواْ عَلَى ٱلۡإِثۡمِ وَٱلۡعُدۡوَٰنِۚ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَۖ إِنَّ ٱللَّهَ شَدِيدُ ٱلۡعِقَابِ ٢
" .........KUMA KADA QIYAYYARKU GA WASU MUTANE TA 'DAUKE KU AKAN BA ZA KUYI ADALCI BA DON SUN TSARE KU DAGA (shiga) MASALLACI (kamar yadda wasu ke taka muku birki wajen aikata abinda ranku ke so wanda ya sabawa koyarwar harka kuce za ku fake da qinsu ku rusa ganin da jagora yayi ), KUYI TAIMAKEKENIYA AKAN AIKIN ALKHAIRI (na hada kan mabiya) DA KUMA TAQAWA (cikin aikin naku) , KUMA KADA KUYI TAIMAKEKENIYA AKAN AIKATA ZUNUBI (na rarraba kan 'yan'uwa) DA KUMA ZALUNCI (wajen yiwa azzalumai aiki da sunan kuna da'awa), KUJI TSORON ALLAH (cikin wannan zagon qasa da kuke yiwa harka), LALLE ALLAH MAI TSANANIN UQUBA NE (ga masu saba masa) ."
(MA'IDAH:2)
Idan muka aikata haka shine mun taimaki jagora cikin da'awarsa, kuma mun sauqaqa masa yadda duk lokacin da Allah yayi dawowarsa cikinmu sai dai ya dora kan abinda ya tarar damu a kansa. Amma idan ba haka mu kayi ba haqiqa mun rusa tubalin da ya dora shi ne, domin in ya dawo sai ya sake sabon gini.
Na'am, komai rusawar da wasu ke qoqarin yi daga cikinmu Allah ba zai hana tabbatar da masu aza wannan tubali yayin da wasu ke rusawa ba.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.
(08137925034)
9th January, 2021/ 26th Jimada-Ulah, 1442.