Nasiha ga matasa 'yan gwagwarmaya!!!


 
@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

ABINDA NA DADE INA ZULUMINSA 

Wannan al'amari yana damuna sosai akan matasan harka, yanzu sun rage himma wajen neman ilimi, iyayen mu (brothers) sun fimu neman ilimi a harka, matasa kuma sunfi iyayen su (brothers) neman aikin gwagwarmaya ba tare da neman ilimin aiki da ita ba.

Misali, wani abu dana fahimta a tare da matasa 'yan gwagwarmaya shine, yanzu kawai idan aka shirya program su ake bari da aikin gyara gurin (programme), su ake bari da shirya fili (decoration), su ne debo kujeru, kawo tabarma da kuma sauran su.

Iya abinda matasan mu suka fi mai da hankali akansa kenan, idan an fito muzahara ma haka za ka gansu a gaba-gaba, sun rungumi wannan aiki sosai tare da nuna cewa su 'yan gwagwarmaya ne amma basu da wani ilimin da zasu iya tafiya da ita harka din. 

Da ace wani yanayi zai bayar ta yadda iyayen mu (brothers) zasu ja baya su barmu da gwagwarmaya, to, da babu wani abin kirki da zamu iya aikatawa a cikinta. Iyayen mu kullum suna kan hanya wajen neman ilimi sun tafi sun barmu a baya.

Mu kuwa matasa gamu nan a gefe, mafi yawanmu ba ruwan su da neman ilimi, sannan ko a jikin su baya damun su tunda iyayen mu suna nema ai shikenan. Majority haka muke yanzu, mu ke a cikin harka amma wani abu da ya shafi zancen ilimi babu ruwan mu da shi, kuma haka matashi zai ce maka ba shi da mai daukan nauyinsa a karatu ne amma yana son yi. Wani abin mamaki kuma akwai waya a hannunsa wacce takai dubu #50,00 kuma da kudin sa ya saye ta.

To, matasa wlh idan zamu tashi mu tashi, domin ita harkar nan dole masu ilimi da aiki ne zasu tafiyar da ita, kuma ilimin shine mafi muhimmanci ga rayuwar mu matasa, domin shine ya tattara komai na rayuwar mu wanda zai kyautata mana dukkanin rayuwa a gidaje biyu duniya da lahira. 

ZANCEN CEWA AKWAI SU WANE DA WANE A CIKIN HARKA DUK BA ZANCEN MU BA NE, KAWAI MU TASHI MU FI SU WANE 'DIN.

Allah ya mana Jagoranci matasa, kuma duk wani aiki da ke kanmu Allah ya bamu ikon saukewa.

~Abubakar Aliyu Ahmad Ningi 

    8th January, 2021.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post