"Kunji Na Rantse Wallahi ba Zanyi Kaffara ba".
_Shaikh Yaqoub Yahya Katsina.
Kunga wannan kashe-kashen wannan sace-sacen, da kwashe Yan Makaranta da akeyi Wallahi ba zai taba tsayawa ba. Duk mai neman tsira da salama domin samun yanci toga Malam Zakzaky (H). Ku shigo Makarantar Malam zakzaky (H), ku zo ku jona sahu bayan Malam Zakzaky (H). Nan ne kawai zaku samu tsira da Mutuncinku. In kun Mutu kuyi Shahada, in kun rayu ku rayu da Izza, karama da Mutunci.
In ka ga dama kace ban da hankali, ko ni mahauka ci ne, amma kana kofar gidanka sai wannan Bala'in ya iske ka na faɗa maka kar kace ban faɗa maka ba.
Waɗanda suke wannan kashe-kashen a Nigeria suke yi a Afganistan Yau Shekara 30 kenan, su ne suke a Syria Yau Shekara 8 kenan, su ne suke yi a Iraqi Shekara 15 kenan, suke yi a Somaliya Yau Shekara 28 kenan, suke yi a Sudan har suka raba ta gida 2.
Shin kana tunani zusu shigo nan Nigeria su bari alhali ga abin da suke so? Gamu da Arzikin Ƙasa Wani Furofesa yake cewa: ai Nigeria babu yadda za'ayi abarta ta zauna lafiya shekara 20, domin in aka barmu zamu fi kowa ce ƙasa Arziki
Ya ku Yan Nigeria in ma wahala kuke ji ma tsoro, to kuna zaune gida zata zo ta cin ma ku tunda ba zaku iya gwagwarmayar Addini musulunci ba. Saboda tsoron wahala ko kisa shiyasa ba zaka bi Addini ba musulunci ba.
To bari kuji yadda Allah Swt ya ce:
"Masu Gwagwarmayar Addinin musulunci ba zasu ji kishin Ruwa ba, ba zasu ji Yunwa ba, ba zasu ji Barci ba, ba zasu ji Gajiya ba, ba zasu taka wani wuri inda Maƙiya basu so su taka ba, face Allah (Swt) ya sanya Mizanin aikinsu mai kyau" ba.
Wanann ita ce Wahala mai Lada, mai Riba mai Lasisi. Wanda ya zaɓi yin wani abu bayan wannan to ya je yayi abin sa zai yi wahala banza ne domin ba ita ce Allah yace ayi ba. Duk wannan Zaluncin da ake yi kune kuka kaisu a wurin har suka samu damar Zaluntarku.
_Shaikh Yaqoub Yahya a wajen Khatamar Maulud Katsina
Asabar 19Dec2020.