A wajan taron mu'utamar Wanda shafin Ma'asumah ta shirya ga wakilanta a ranakun 1, 2 da 3 ga watan Janairu, 2020, wanda ya gudana a garin Shinkafi karo na uku. Ma'asumah Radio ( sashen gidan Radio na Ma'asumah) ta fitar da wasu gwaraza daga cikin ma'aikatan na gaba daya shafin Ma'asumah ta karramasu da shaidar girmamawa domin yabo da karin karfin gwiwa bisa jajircewarsu.
Daga cikin wadanda aka karrama din akwai;
- Shahid Ishaq Sulaiman
- Mas’udu Dan masani Shinkafi
- Naziru Sa'idu Gusau
- Munauwar Mukhtar Gusau
- Ammar Usman Sabo
- Malam Ado Isah Guda
- Basiru Haruna Sigau
- Abubakar Labbo Shinkafi
- Abbakar Ibraheem Kudan
- Zaidu Sulaiman Kano
- Yahya Isah Muslim
- Mahdy Tukur Almizan
- Jibril Usman Sarki
- Khadija Lawal Daura
- Fatima Khazimiyyah
Duk wadannan zababbun gwararazan da sashen gidan Radio na Ma'asumah ne yayi dubi ya tantance su ya karramasu bisa kwazo da kokarinsu wajan aiki tukuru ga wannan shafi domin amfanuwar al’umma. Karramasu da ayi bashi ke nuna cewa sune kadai masu bada gudummawa ba, kowanne daga cikin wakilan Ma'asumah gwarzo ne kuma abin karramawa da yabawa.
Muna fatan Allah Ya karawa dukkanin kwazo da jajircewa wajan sadaukar da dukiya, Ilimi, Tunani, Lokacin domin cigaban al’umma alfarmar Sayyada Fatima Ma'asumah (a.s). Allah Ya tabbatar da ayyukanmu bisa mizani na Ikhlasi.
Daga shugaban gudanarwa na sashen Ma'asumah Radio ‘Abbakar Ibraheem Kudan’ a madadin dukkanin ma'aikata.