_*Ma'asumah Nigeria News Updates*_
Tun Jiya Jami'an Tsaro Suka Tafi da Mutum (2) daga Cikin Almajiran Mlm Zakzaky (h) Na Garin Shinkafi Dake Jihar Zamfara Biyo Bayan Yin Zanga-Zangar Da Mutanen Garin na Shinkafi Sukayi Bayan Garkuwa da Wani Matashi da Mahara sukayi a Daren Assabar 02-01-2021 , Inda Mutanen Gari Suka Nuna Rashin Amincewar su Akan Daukar Wannan Matashi Da Akafi Sani da Isma'ila Laga, Yana daya Daga cikin Almajirin Sheirk Ibraheem Zakzaky (h) Na Wannan Gari, Wanda A Bangare Guda Ya Zamo Garkuwa Kuma Jarumin Matashi mai Kishin Kansa da Al'ummarsa.
Fusatar da Al'ummar Garin Shinkafi Sukayi Akan Barin Wadannan Maharan Suna Cin Karen su ba Babbaka bayan Sulhun Da Gwamnatin Jahar Tayi Dasu, Yasa Suka Fusata Akan Rashin Amincewar su da Daukar Dai-dai da Maharan ke yi musu, Inda Majiyarmu ta Tabbatar Mana Cewa Sunfito Zanga-Zanga Domin Bayyana Fushin su Ga duk Wani mai Fada aji na Garin na Shinkafi, inda wasu sukayi Fashe-Fashe Kafin Daga Bisani a Sako Jarumin da Maharan Suka kama.
Wannan Abun da Al'ummar Garin Shinkafi Sukayi Yabar Baya Da Kura, Inda daga Baya Muka Samu Sanarwar A Jiya Litinin 04-01-2021 Anbi Almajiran Na Mlm Zakzaky (h) Ana Kamu Wanda Suka Hada Da Falalu Hassan Tare Junaidu Almajir,
Har Zuwa Yanzu da Muke maganar nan Suna Hannun Jami'an Tsaro.
Tambayar Da Al'ummar Garin Shinkafi Suke yiwa Kansu Shi ne miya Hada Kama Wadannan Mutane da Wannan Rikici, Ko Anason A Rura Wutar Rikicin Addini ne A garin?
Zamu Zura Ido Domin Bibiyar Abunda ke Faruwa. kuci gaba da Kasancewar damu da Wannan Zalunci da Azzalummai Suke Shiryawa akan Wadannan Bayin Allah....
Kamarawa
ReplyDelete