@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
Sanin kowa ne cewa shi maqiyi ba abokin mu'amala bane, sannan a ko da yaushe a kanyi taka-tsan-tsan cikin lamarinsa bisa qoqari na kaucewa sharrinsa ko makircinsa.
A ko da yaushe burin maqiyinka shine yaga wani sharri ya same ka cikin komai naka na rayuwa. Wannan abu kuwa zai iya kasancewa cikin dukiyarka ko iyalinka ko kuma wajen mu'amalarka da jama'ah. Sai dai kuma gazawar maqiyi shine bai isa cutar da kai a lahirarka ba.
Idan kuwa hakane za mu iya cewa duk wani abu wanda zai iya zama sanadin cutuwarka a lahira shine babban maqiyinka.
Imam Ja'afarus-Saadiq (A. S) yayi bayani cikin wani hadisi kamar haka,
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
Ya zo cikin Kafiy daga Muhammad Bn Yahya, daga Ahmad Bn Muhammad Bn Isah, daga Ibn Mahbubin , daga Abu Muhammad Al-Waahibeey yace: Na ji baban Abdullah (A. S) yana cewa;
الكافي عَنْ مُحَمَّدِ بْنِ يَحْيَى عَنْ أَحْمَدَ بْنِ مُحَمَّدِ بْنِ عِيسَى عَنِ ابْنِ مَحْبُوبٍ عَنْ أَبِي مُحَمَّدٍ الْوَابِشِيِّ قَالَ سَمِعْتُ أَبَا عَبْدِ اللَّهِ ع يَقُولُ
" KU TSORACI BIN SON ZUCIYARKU KAMAR YADDA KUKE JIN TSORON MAQIYANKU, DOMIN BABU WANI ABU MAFI TSANANIN GABA GA MUTUM KAMAR BIN SON ZUCIYA DA KUMA ABINDA HARSUNANSU KE GIRBA ."
احْذَرُوا أَهْوَاءَكُمْ كَمَا تَحْذَرُونَ أَعْدَاءَكُمْ فَلَيْسَ شَيْءٌ أَعْدَى لِلرِّجَالِ مِنِ اتِّبَاعِ أَهْوَائِهِمْ وَ حَصَائِدِ أَلْسِنَتِهِمْ[42].
(1) الكافي ج 2 ص 137.
A yanzu haka idan mutum yasan wane maqiyinsa ne na zahiri za kaga yana taka-tsan-tsan da shi, domin ya san matuqar ya sami dama zai iya cutar da shi, amma fa cutar takan tsaya iya nan duniya ce.
Ita kuwa bin son zuciya shirka ce, domin a koda yaushe burinta shine taga ta baka wani aiki wanda ke cin karo da umarnin Allah, ma'ana ka biye mata ka saba umarnin Allah.
Shine a wani guri Allah (T) ke cewa,
" ASHE BA KAGA WANDA YA RIQI BIN SON ZUCIYARSA ABIN BAUTARSA BA .....?"
Kenan bin son zuciya yiwa Allah kishiya ne, kuma wanda ya yiwa Allah kishiya ba shi da rabo a lahira. Wannan na nuna mana ne cewa bin son zuciya ya fi mummunan hadari (risk) wajen fuskanta fiye da fuskantar maqiyi na zahiri.
Subhanal-Lah ! Sai dai har yanzu mutane basu san ko gane babban maqiyinsu wanda ya kamata suyi gaba da shi ko su nisance shi ba.
To, Imam Sadiq (A. S) ya haskaka mana, yanzu kawai ya rage gare mu ne.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.
(08137925034)
8th January, 2021/ 25th Jimada-Ulah, 1442.