A cikin bayanin, malaman na yankin Jabl Amil yanki mai tarihin ilimin addini a tsawon tarihi, sun bayyana fim din da aka shirya akan Fatima Zahra (AS) wanda wani mutum mai suna Yasir Habib da ke yin shigar addini ya jagoranta, da cewa wannan fim din baya wakiltar mabiya mazhabar ahlul bait.
Bayanin ya ce, a zahirin fim din an nuna cewa ana magana ne akan Sayyida Zahra amincin Allah ya tabbata a gare ta, amma hakikanin abin da ke ciki baya da sahihanci ko asasi, kuma manufar hakan ba bayyana matsayin Fatim Zahra ba ne, yunkuri ne na kawo fitina a tsakanin musulmi.
Tun kafin wannan lokacin dai manyan malamai a cikin kasashen Iran da Iraki da Lebanon, sun zargi wanann mutum mai suna Yasir Habib da yake zaune a birnin London, da yin aiki da ya yi daidai da manufofi na hukumomin leken asiri na Burtaniya da wasu kasashen turai, inda yake amfani da sunan mazhabar Ahlul bait wajen bata sunan addinin musulunci.
Bayanin ya kirayi sauran malamai dam asana da kuma masu hankali a cikin al’ummar musulmi, da su hattara da irin wadannan mutane masu kokarin aiwatar da wata manufa ta rarraba kan musulmi da kuma haifar da fitina a tsakaninsu, a daidai lokacin da musulmi suke butar hadin kai fiye da kowane lokaci, domin tunkarar kalubale da ke a gabansu.
Source:-Tehran (IQNA)