Khadija lawan daura ✍️
Hakika ranan juma'a ranache wadda tayi dai-dai da 1/1/2021 mun Kama hanya Daga Daura zuwa mu'utamar a garin Shinkafi ta jihar Zamfara.
Nida wasu ba'adin Yan uwana na Addini Wanda suke kere Yan Uwan jini a wurina.
Mun tafi chikin Aminchi, da Farinchiki, da Soyayyar juna.
Chikin iyawar Allah, muka Karasa garin Gusau, inda daga Nan muka hau motar garin Shinkafi Mai tsan-tsar Albarka.
Isarmu keda wuya muka Karasa masaukin mu, inda muka fara haduwa da maban-bantan tarba da karramawa.
Babban Abunda ya burgeni ta yanda Dan Uwa Abinsa Bai dameshi ba kowa so yake yaga Dan uwansa chikin buqatar wani Abu Dan yayi Masa.
Tabbas munga karramawa,munga mutuntawa,munga soyayya.
Muna fatan Allah ya sakama Yan Uwan da sukayi dawainiya da Alkairi.
Ina Miko jinjinata ga MAS'UD DANMASANI SHINKAFI dama sauran Yan uwa na garin Shinkafi dama mahalarta taron gaba daya.
Ina Kuma Miko sakon godiya ga Malan Ammar Usman Sabo bisa wasu hidimomi da ba saina Anbata ba.
JINJINA TA MUSAMMAN GA FARINCHIKI MU HASKEN IDANUNMU JIGON RAYUWAN MU SAYYID IBRAHIM ZAKXAKY (H).
Hakika duk wata soyayyar da kulawa da muke nuna ma junanmu sune sular hakan Kuma sune sular shiriyarmu Allah ya kwato mana su Sayyid Allah ya Basu lafiya.
AMINCHIN ALLAH YA QARA TABBATA GA TSOKAR JIKIN MANZON ALLAH SAYYIDA MA'ASUMA (s.a)
WASALLAHU ALA MUHAMMAD WA ALIHID-DAYYIBINAD DAHIRIN❣️