____
Na Samu Chaji Imani Yayin Danaje Dubiyar Dan Uwa Falalu Hasan A Assibiti
Bayan Kama Dan Uwa Falalu Hassan Biyo bayan Zanga-Zangar Da Mutanen Garin Shinkafi Sukayi Domin Fusata akan Maharan dake Masu Dauki Dai-dai A Garin, Sanadiyyar Kama Wani Jarumin Matashi Da Akafi Sani da Isma'ila Laga Da Maharan Suka Kama a Ranar, Inda Aka kama Mlm Falalu Hassan Da Junaidu Almajir Bisa Zargin Kage da Sharri Da Ake Tuhumar su Dashi,.....Sanadiyyar Kamun Ya Tayar da Rashin Kadiyar mlm Falalu Hassan Inda Ya kwanta Assibi Tsawon Kwana Ukku Yana Karbar Magani Tare da Rakiyar Jami'an Tsaro domin Kula dashi A Matsayin Sa Na Wanda Ake Tuhuma.
____
Bansamu Ziyarar Assibitin Ba Sai A yau da Misalin Karfe 5:50 na Yammacin Yau Alhamis, Da ni da Dan Uwa Ashafa M. lawal, Bayan Shigarmu Mukabi Sashen da muke Tunanen Yake bamu sameshi ba Sakamakon Gyaran Assibitn Da Akeyi, Chan Muka Hangi Wasu Gungun Majinyata A Zaune muka dan Matsa kadan Domin Tambayar Su, Bayan Gaisawa, Muka Tambaye su....Tambayar su keda wuya Sai Suka Ce :- "Ai Tunda Safe Yayi Mana Sallama Yace Idan Jami'in Tsaron Dake Tsaro na, Idan Yadawo A Gayimai Ya sameshi a Police Station shi ya Warke..
Koda Jami'in Tsaron Yadawo Ya Tambaye mu Cikin Tashin Hankali Sai Muka Ce mishi Yace Kasameshi a Police Station shi ya Warke, A Lokaci Guda Dan Sanda ya Cika da Mamaki Tare da Furta wata Alfasha Ta Mamaki *(Bura Uba)* Wa'iyazu Billah, Ya jinjina kai Tare da Cewa Wannan Mutum Jarumi yake.........Da Sauran hirar Da mukayi da Wadannan Mutanen Majinyata...
Lalle nasamu Charjin Imani A Wannan Ziyarar duk Da bamu Samushe ba Amma Munji Abubuwa...