KOKARIN HAIFAR DA RIKICIN ADDINI


KOKARIN HAIFAR DA RIKICIN ADDINI||“Makirci ne ganin Shari'ar Su Malam Zakzaky (H) ta ƙarrabo”. 


•••Inji Shaikh Yakubu Yahaya Katsina yayin da ya ke bankaɗe sabon makircin jahiliyya ga Harkar Musulunci a jiya Juma'a 15/1/2021.


“Azzalumai na nan suna ta abinda suke yi ko? Eh!  Mugayen bayi, Allah Ka murƙushesu, Ka kawo ƙarshen zalinci da azzalumai. 


Sun ce wai za a yi rikin addini a jahohin Katsina,  Kano da Kaduna, da Sokoto da Jos... Wai sun gano za a yi rikicin addini. Anya ba dai su ne zasu haifar da rikicin ba, ina jin su zasu haifar da rikiin addinin, dan an saba yin haka nan, tsohon yayi ne ma wannan an saba yin wannan. 


Lokacin na san gabas ta tsakiya da yake lokacin suna da ‘interest’ da gabas ta tsakiya,  sai kaji sun ce bom zai tashi, wai jami'an leƙen asiri sun gano za a tada bom a wuri kaza, to kuma sai kaji bom ɗin ya tashi. To wa ya ɗana bom ɗin?. 


To wanda ya gano hayaƙi shi za a ce ya ɗebo wuta ko ma shi ya kunnata, hmm... Zaku ce rikicin addini, rikicin addini a wane salo? A ina ta ina? Wanene ke ƙoƙarin maida waniii... Iyakar saninmu rikicin addini shi ne ace Musulmi na son ya maida kirista Musulmi ko kuma kirista na son ya maida Musulmi Kirista, shi ne rikicin addini, (wani mai addini ya ce zai maida wani mai addinin a addininsa da ƙarfin tuwo) shi muka sani rikicin addini. 


Su dai su ce ƙasa ta suɓuce masu, linzami ya kuɓuce ta kwaɓe sun rasa yadda za su yi da mutane saboda haka bari su ƙirƙiri rigimar su buga mata tambarin addini... Yawwa haka zaku ce. 


Sai mu ce mun rasa yadda zamuyi da ƙasar nan muna tafiya a iska bamu san ina zamu ba,  koomi ya lalace ya ruɗe ya rikirkice bamu san ya za a yi ba, to yanzu ’yan kasa sun sa ido su ga ya za a yi, sai a ce a ƙirƙiri rigimar addini,  ace rigimar addini ake yi (amma rigimar siyasa ba rigimar addini ba ce) ba wani rigimar addini a ƙasar nan. 


Rigingimun ƙasar nan sunansu rigingimun siyasa da sunan addini, yawwa, kuma bani tsammanin wani mai hankali mas'uli Amamallah (za'a tada shi gaban Allah a tambayeshi,  zai shiga cikin wannan rigingigimu. Tana iya yiwuwa kuma akwai abinda suke son su cimmawa, kaga kamar kafin su yi waki'ar Zariya wasu sojojin amerikawa an ga suna ziyartar Malamai hada wani Malami ga hotonsa nan suna gaisawa sun kai masa ziyara a gidansa... To kuma kwanan nan kuma anji yana ta ɓaɓatu yana ta maganganu yana cewa; ’yan Shi'a, Iran zata zo ta taimaki Najeriya, yaushe ne, wanene... Ya ce wai Shugaban ’yan Shi'a ya maida mata karuwai, ya yara matasa suna alfasha tsakaninsu da junansu, yana kaza yana kaza... Surutai nazautuwa, na rashin kan gado, na rashin hankali na rashin balaga shekaru ma. 


Wato ina ga amerikawan haka suka gaya masa ya faɗa, shi kuma da yake ba ya da wayau, Hmmm. 


Kuma suka ce wai kwanan nan za a kashe wasu ba’adin Malamai.  To har ma naji wani yayo katoɓara ina ji ƙila asirin da aka yi da shi ne aka tattauna aka ce ai ga yadda za a yi ga yadda za a yi.  To sai ana yi masa complain, ina ji ko game da Malam Abduljabbar ne?... Yawwa sai yana magana (ga wani irin Hausa nasa) “ai wannan kashe shi kawai za a yi kawai sai a huta” shi mai tambayar ya ke cewa “ba ku kira shi ku zauna da shi ku tattauna ku fahimci juna?” sai ya ce “a'a ai wannan kasheshi kawai za a yi a huta”. Sai ta kuɓuce masa maganar, ina tsammanin hakanan... 


Akwai wani ma cikin karnukan farautarsu amma shi ba ɗan wannan ƙungiyar ba ne shi ma yayi nasa amma audio ne, shi yayi, shi ma yayi maganganu. To duk dai abinda muka fahimta shi ne suna son su haifar da rigingimu musamman ganin cewa Shari'ar su Malam ta ƙarrabo, to ya za a yi su haifar da rigimar da za ta hana shara'ar ko kuma su dawwamar da Malam a tsare, Maganar kenan. 


Ko kuma ya za a yi su haifar da rigimar da zata dawo ma harka ɗin baki ɗayanta tunda sun ce ba matsala kamar yadda asirinsu ya bayyana kwanan nan; wai an gano ba matsala cikin harka, shi ne wai su ke son yanzu kuma su samar da irin wannan matsala ɗin. To shima wancan ɗin da aka ji yana maganganu da alama abinda suke so shi ne su maimaita irin na Sokoto na Ɗan Mai Shiyya, lallai abinda suke so suyi kenan.  Shi wannan da aka ji shi a audio yana ɓaɓatu ko da yake dama ya saba yana ɓaɓatu irin waɗannan maganganun masu kama da irin waɗannan shi ma ƙarshenta zasu so ne su kawar da shi. 


 Shi ma wannan da yake maganar za a kawar da Malamak ko ’yan shi'a suna kaza,  shugan 'yan shi’a ya yi kaza, sharri iri-iri (bidiyo ne ma shi na wannan na Jos ɗin) wai kuma a Masallacin Juma’a. To kaga wala'alla su za su dawo ta bayan fage su kawar da shi ko su kawar da wancan duk da ban-bancin ƙungiyoyinsu da da fahimtarsu amma sunyi ittifaƙi akan ƙiyayya da gaskiya (sun haɗu akan ƙiyayya da Malam da fikirarsa.  To kaga tunda su mahukunta ba su da abinda ya wuce wannan sai su zo su kawar da sh sai suce ai ’yan shi'a sun kashe Malam wane ko sun kashe Shaikh Wane, to ta Allah ba tasu ba mu dai HASBUNALLAHU WA NI'IMAL WAKEEL”... 


Rubutuwa:- Bin Yaqoub Katsina

Asabar16/1/2021.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post