Rbtw: J. I. R
Allah ya kawo mu goben da Zainab ta ambata ga kawarta Fateema, don bata labarin da ta kunso a matsayin tsaraba.
Zainab ta yi wanka, ta yi kwalliya ta fito zata tafi gidan su Fateema, Zainab: "Umma to zan tafi gidan su Fatima don in gaida mamansu, kar ta ji labari na dawo ban je na gaisheta ba". Umman su Zainab sai ta ce: "To Zainab sai kin dawo ki gaishe min da maman Fateema. Zainab ta fita ta nufi gidan su Fateema.
A hanyarta sai ta yi karaf- caf da tsohon saurayinta Ahmad. Ta tsaya kamar ta masa magana, ta kallesa. Shi ko ko kallonta baiyiba, ya bar wurin ma don kar ta masa magana. Haka nan dai Zainab ta wuce cikin bacin rai don irin basar da ita da Ahmad yayi.
Bayan isarta gidan su Fateema; Fateema ta kaita dakinsu, ta ibo ruwa ta kawowa Zainab. Bayan ta gama cikin raha ta mamaki! Ta ce: "Amma kawata Allah kauyen nan ta amsheki, ban labari ko dai akwai wani sirri ne?", Zainab ta yi dariya ta ce, "Ai Fateema akwai sirri kam, na yi kasuwa a kauye". Cikin mamaki Fateema ta ce, "Kasuwa kuma Zainab?, wana irin kasuwa?", Zainab, "Kwantar da hankalinki kawata zaki ji labari".
Zainab ta fara baiwa Fateema labari, "Ai na fada miki zuwana kauyen nan arziki ne, na hadu da wani babban alhaji ya ce yana so na, da ban amsa masaba. Sai kuma naga ba mai kin arziki sai matsiyaci, shi ne amsa masa. Ina fadi miki duk zuwa sai ya ban 30k, kuma ya kan zo a sati sau uku, gobe ma mun yi waya zai zo ya gabatar da kansa ga Umma". Fateema budan bakinta ta ce, "Gaskiya baki kyautawa Ahmad ba, ki duba irin kular da Ahmad ya baki, Zainab wana uzuri ne ya ta so ki fadawa Ahmad bai miki duk da shi ba dan kowa ba ne? Kar ki manta so fa, yanzu ke a tunaninki kudi shi ne so?, Ya kike tunani a ce wancan ya rasa dukiyar da ya ja ki, ko yaya kike tunani ke ki samu wata jarabawa kyan da kike dashi ya gushe, ya kamata ki sani mai kyautata ma don Allah shi mai sonka. Kowa ya sani Ahmad masoyinki ne, duk wata kulawa da kike bukata ya baki, Zainab! Irin sakayyar da zaki masa kenan ta cin amanarsa, to wallahi in har Ahmad bai yafe mikiba zaki ga sakayya domin cin amana ba wasaba".
Zainab dai jikinta ya yi sanyi game da irin maganganun da kawarta ta fadi, ta tashi cikin fushi ta fita ta yiwa maman Fateema sallama ta tafi gida. Ta je gida ta shiga daki tana ta tunani game da maganganun da Fateema ta fadi mata.
Mu hadu a kashi na gaba....