Jawabin Shaikh Zakzaky A Ranar Mauludin Sayyida Zahra (S) 1436H
Rubutawa: - Cibiyar Wallafa
'Yan uwa Musulmi Assalamu alaikum wa Rahmatullahi Ta’ala wa Barakatuhu
To, yau rana ta farko na jerin ranekun bukukuwan Mauludin Sayyidati Nisa’il Alamieen, Sayyida Fatimatuz-Zahra Salamullahi Alaiha. A shekarun baya mun saba mu kan kwana uku ne a jere muna yi, amma wannan shekarar saboda yanayin da ya zo ana zabe ya sa ba zai yiwu mu samu kwana ukun kamar yadda muka so ba...
Maulud din Sayyida Zahra yana daga cikin abin da yake na nuna soyayya ga Ahlulbaitin Nubuwa, wanda ake farin ciki da farin cikinsu, da bakin ciki da bakin cikinsu. Kwanan nan muka yi zaman jaje na ranar 3 ga watan Jimadal Ula, kafin nan ma mun yi zaman jaje a watan jiya, na lokacin wafatinta. To, yanzu kuma daidai wannan lokacin murnar haihuwarta ne.
Kamar kullum, mu kan so mu dan kawo wasu ruwayoyi don tunatar da juna dangane da abin da ya shafi haihuwar Sayyida Zahra wacce aka Haifa ranar 20 ga watan Jimada Assaniya, zai kasance bayan aiko Annabi ko da shekara uku ko da shekara biyar. Kamar yadda za mu gani a ruwayoyi daban-daban, idan ya zamo da shekara uku ne, kaga bayan shekara goma kenan yayi hijira, shi yasa na shekara biyar zai fi kama, don in aka ce bayan shekara biyar da aike (aka haifi Sayyida), tunda Manzon Allah yayi shekara 13 ne a Makkah sannan yayi hijira zuwa Madina, in ya zama shekara ta biyar ne, kaga an yi hijira kenan tana da kamar shekaru takwas, kuma aurenta ya kasance bayan Hijira da kamar shekara guda, sannan kuma bayan wafatin Annabi ba dadewa ya kasance nata wafatin, saboda haka duka kaga ta yi shekaru 18 ne a duniya.
To, haihuwar Sayyida Zahra a Makkah bayan aiko Annabi ne. Wannan hatta ruwayoyin sauran mutane basu samu sabani dangane da shi ba, illa su ce shekara uku bayan hijira, ko shekara biyar bayan hijira. Inda suka zo suka yi wasa da tarihi, shine inda suka yi kokarin su nuna akwai wadansu ‘ya’yan Manzon Allah mata wadanda wadansu manyan mutane suka aura. A nan ne wasa da tarihi ya zo.
Domin idan muka tambaye su, yaushe aka haifi Sayyida Zahra? Za su ce bayan Hijirar Annabi (S). Da wane lokaci? Za su ce imam bayan shekara uku ko bayan shekara biyar. Akwai ruwayar cewa an haifeta kafin a aiko Annabi? Za su ce maka babu. To shikenan, zance yak are, kaga a nan ba wani rigima kenan, wannan muna iya cewa an samu ittafaki. Inda suka yi wasa da tarihi to nan ne ya sabawa hankali. Inda suka ce akwai ta da kanne mata wadanda aka haife su bayanta.
Don ittifakan Manzon Rahma (S) dansa na farko sunansa Alkasim, kuma su Larabawa su kan yi wa mutum alkunya ne da sunan dansa na fari. Shi yasa ake ce masa Abulkasim, saboda haka Alkasim shine dan Manzon Allah na farko. To, yaushe aka haife shi? Shima bayan aiko Annabi ne, tunda ya rasu yana karamin yaro ne, kuma bayan rasuwarsa ne ma suka yi murna a Makkah suna cewa bashi da magaji. Har ma wani makiyin Annabi ya kira shi da Abtar (Mai yankakken baya). Yace ku kyale shi, Abtar ne, in ya mutu shikenan bashi da dan da zai gaje shi. To, shine Allah Ta’ala ya saukar masa da sura;
Bismillahir Rahmanir Raheem
Inna a’adainakal khauthar, Fasalli li-Rabbika wanhar, Inna shaani’aka huwal Abtar.
Mun baka Kauthar. Kalmar Kauthar wacce ta fito daga ‘Ka-tha-ra’ wato Yawa. Suna cewa ma’anarsa alkairi mai yawa. Wato Allah ya ba Annabi mai yawa na alkairi. Kuma ittifakan akwai korama na Alkausar wanda mutanenmu suke ce masa Kausara, suna cewa Tafkin Kausara. To, akwai Alkausar na tafki, wato korama, wacce take korama ce a Aljanna, amma za a hudu da bangarensa a filin Kiyama a yayin hisabi, wanda a rannan kowa yana kishi sai wanda zai sha daga wannan Alkauthar din. Wanda ruwayoyi dangane da Alkausar ya yawaita.
Sannan kuma wata fassara dangane da Alkauthar ita ce Sayyida Zahra (SA). Ita ce Khauthar, daga cikin sunannakinta. Ita ce aka ba Manzon Allah (S), tunda an ce; Inna a’adainakal khauthar, Mu mun baka Khauthar; Fasalli li-Rabbika wanhar, Kai sallah ga Ubangijinka kai suka (ka yi sallah da yanka); Inna shaani’aka huwal Abtar, Makiyinka shine yankakke (shine zai zama bashi da aqiba).
To, kuma tunda idan ana so a lallasheka za a lallasheka ne da abin da ya dace da abin da aka maka gori. An wa Manzon Allah gori ne kan bashi da da, dansa na miji ya rasu, saboda haka bashi da magaji. To, sai Allah (T) yace masa kar ka damu, makiyinka ne yankakke, ma’ana kai ba yankakke bane. Saboda mene? Mun baka Khauthar. To, ka ga dole Khauthar din nan yana nufin Da ne.
In ba haka ba ai ba a lallashinka kana bin da akai maka gori a kansa da wani abu daban, na kan ba da wani misali, nace da ace wani zai maka gori yace baka da mota, sai wani yana so ya lallashe ka yace manta da shi. Ya ya kamata yam aka? Ya baka mota ‘yar ubanta. Yace kyale shi nan shima da yake da qajaga, kai ga sabuwa nan. Idan kuwa misali aka ce yam aka gori baka da mota? Ga fura ka sha. Manta da shi kawai. To ta ina fura zai lallashe ka a kan kai da aka ce baka da mota?
To, tunda aka wa Manzon Allah gori a kan bai da Da. Sai Allah Ta’ala yace manta da shi, makiyinka ne yankakke, Mu mun baka Khauthar, to Khauthar din nan it ace Sayyida Fatimatuz Zahra. Ita ce kadai take da matsayin Asiba a cikin ‘ya’ya mata gaba daya. Ita ce kadai ke da matsayin Da namiji. Da ruwaya tabbatacce, Manzon Rahma (S) yana cewa; “Duk abin haihuwa ana jingina shi da mahaifinsa ne, sai ‘ya’yan Fatima, ‘ya’yan Fatima ‘ya’yan uban Fatima ne.”
Za mu cigaba.