@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
ADALCI NA DAGA CIKIN SIFFOFIN ANNABAWA (A. S)
Adalci siffa ce ta Allah (T) kuma siffa ta Annabawa (A. S) wacce ake samunta ga dukkan mumini da mumina.
Da shike wannan siffa ta kebanta ne ga bayin Allah salihai za kaga ana rasa ta cikin wasu masu amsa sunan malantaka da kuma mafi yawa daga cikin shugabanni .
Duk wanda aka same shi na aikata adalci, to, za kaga yana da matsayin mai girma wajen jama'a, ko da kuwa su ba sa yin adalci ga mutane.
Ya zo cikin Amaliy lis-Sudduq, daga Imam Sadiq (A. S) yace, Manzon Allah (S. A. W. W) yace,
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
" MAFI ADALCIN MUTANE SHINE WANDA YA YARJEWA MUTANE (irin) ABINDA YA YARJEWA KANSA, KUMA YA QYAMACE MUSU (irin) ABINDA YA QYAMACEWA KANSA ."
الأمالي للصدوق عَنِ الصَّادِقِ ع قَالَ قَالَ رَسُولُ اللَّهِ ص أَعْدَلُ النَّاسِ مَنْ رَضِيَ لِلنَّاسِ مَا يَرْضَى لِنَفْسِهِ وَ كَرِهَ لَهُمْ مَا يَكْرَهُ لِنَفْسِهِ[8].
Ma'ana, wanda yafi kowa adalci shine wanda yake sowa mutane irin abinda yake sowa kansa na alkhairi, kuma ba ya so yaga wani abu na sharri ko baqin ciki ya sami mutane kamar dai yadda shi ma ba ya son irin wadannan abubuwa su faru a kansa.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.
(08137925034)
2nd January, 2021/ 19th Jimada-Ulah, 1442.