KO ABINDA GWAMNATIN JIHAR KADUNA TAYIWA MASU KARATUN AL-QURA'ANI GIRMAMAWA NE KO WULAKANTA MUSULUNCI?

 Yadda Gwamnatin Kaduna ta rika wulakanta masu karatun Alkur’ani mai girma a Zariya

Jami’an tsaro sun rika yi wa al’umma kwacen waya


Daga Ammar M. Rajab


A yau Litinin 18 ga watan Janairun 2021, gamayyar jami'an tsaron da ya hada da Soja, ‘yan sandan kwantar da tarzoma (Mopol), ‘yan sanda, ‘yan banga, KASTELEA tare da kuma jami'an gwamnatin Kaduna sun rika sintiri a garin na Zariya sun kwamushe masu karatun Alkur’ani mai girma bisa tsarin allo.


Jami’an sun rika yin samane suna cafke dukkannin masu karatun Alkur’ani mai girma na Allo wadanda aka fi sani da Almajirai. Shi dai tsarin Almajirci ya fi shahara a tsakanin mabiya Darikar Tijjaniyyah, inda suke koyar da littafin Allah wato Alkur’ani mai girma da irin wannan tsarin.


Sai dai da safiyar yau ne jami’an suka rika bi tituna a garin Zariya suna kamen duk wani wanda suka ga ya yi kama da almajiri.


Tawagar jami’an tsaron sun yi dirar mikiya a Unguwan Tudun Jukun dake Zariyar, inda suka dira a wata makarantar Allo dake kusa da makarantar Firamaren Unguwar. A makarantar sun tafi da Malami daya da almajiri daya sakamakon duk almajiran makarantar sun fita wasu kuma sun ranta ana kare.


A karshe jami’an sun bar sakon cewa a maida duk almajiran dake makarantar zuwa garuruwansu domin kaucewa fushin hukuma.


Har wala yau a lokacin sintirin, Wakilinmu ya labarto mana cewa; duk almajirin da aka kama suna saka shi a doguwar mota ce. A yayin da kuma mutanen gari suka rika dafifi suna kallon ikon Allah da tofa albarkacin bakinsu.


Har wala yau jami’an tsaron sun rika kwacewa wadansu al’umma wayoyinsu a daidai Agoro dake Tudun Wadan Zariya, inda kuma har ya zuwa hada wannan rahoton ba su maida wa kowa wayarsa ba.


Idan ba ku manta ba a makon da ya gabata, jami’an tsaron suka afkawa makarantar Sheikh Dahiru Usman Bauchi, inda suka kwashe almajiransa. Sai dai ko da BBC ta tuntuɓi gwamnatin Kaduna, Manjo Garba Yahaya Rimi, shugaban hukumar kula da ababan hawa da muhalli ta jihar Kaduna, KASTELEA, kuma shugaban kwamitin yaki da annobar korona a jihar ya bayyana cewa kai samamen na daga cikin matakan da suka fara ɗauka na daƙile annobar korona.


Ya kuma bayyana cewa wannan matakin ba wai ya tsaya bane kan makarantar Sheikh Dahiru Bauchi kaɗai, inda ya ce ya shafi dukkan ƙananan hukumomi 23 ne na jihar.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post