An Ƙarfafi ‘Yan Midiya Tare Da Gargaɗin Su Kan Saƙonnin Da Suke Yaɗawa A Zaurukan Sada Zumunta.
An ƙarfafa tare da gargaɗin masu ta’ammuli da rubuce-rubuce a zaurukan sada zumunta na zamani, har ma da ‘yan jarida, dangane da rubuce-rubuce da sauran sakonnin da suke yaɗawa al’umma.
Shahararren Malamin addinin musuluncin na ɓangaren ‘yan uwa Musulmi Almajiran Shaikh Ibraheem Yaqoub Zakzaky a Katsina, Shaikh Yakubu Yahaya ne ya yi wannan kwaɗaitarwar da kuma tsoratarwar lokaci guda, a yayin da wata tawaga ta masu ta’ammuli da zaurukan sada zumunta na zamani ( ‘yan midiya) da ‘yan jarida suka kai masa wata ziyara a ranar Lahadin nan.
Malamin ya ce; “Shi wannan ɓangare na Midiya, ɓangare ne mai matukar muhimmanci. Domin da shi ne ake juya duniya, har ma yana cikin rukunnan gwamnatocin zamani; Majalissar zartarwa, Majalissar dokoki, ɓangaren Shari’a, sai na hudunsu Midiya. Da su ake tafiyar da gwamnatocin duk duniyar nan.” In ji shi.
“Amma ku (‘yan midiya) ba ƙarya za ku yi ba; ba kuma ƙage za ku yi ba; ba kuma don ba ku son mutum za ku fadi abin da bai fada ba. Allah na cewa; “Kada ƙiyayya da mutane ta sa ku yi masu rashin adalci, ku faɗi abin da yake daidai shi ne abin da ya fi zama kusa da Taƙawa…” alamar kana jin tsoron Allah kenan. Saboda in ka faɗa; za a tambaye ka; in ma ka rubuta; za a tambaye ka!” Ya tsoratar.
Malami Yakubu Yahaya ya kuma jinjinawa ‘yan midiya musamman masu isar da saƙonnin addini a zaurukan na sada zumunta, inda ya yaba masu matuka, ya kuma ƙarfafa masu gwiwa kan haka.
“Kar ku raina abin da kuke yi, yana da muhimmanci. Allah ya san shi, kuma yana aiki da shi( wajen ɗaukaka addininsa).” Ya kwaɗaitar.
“A sa hotuna na gaskiya, maganganu na gaskiya a sa wa mutune su gani. In bidiyo ne, a sa wanda zai zama ya amfani jama’a, har su tsaya su gani.” Ya nasihantar.