Imam Ali (a.s) ne tutar dake tsakanin Allah (T) da halittun sa !!!



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED 





BABU MAI YIN SHAKKA KAN HAKA SAI DAI MUSHIRIKI 


Shi Allah (T) yakan ajiye baiwarsa ce a inda yake so kuma kan wanda yake so ba tare da jin tsoron mai zargi ko qaryatawa ba, kuma ba ka iya tuhumarsa dalilin hakan ba. 


Bayan Manzon Allah (S. A. W. W) babu wata halitta wacce ta kai matsayin Imam Ali (A.S) a wajen Allah (T) .  An sami fifiko ma tsakanin Manzannin Allah (A. S) ba tare da wani daga cikinsu ya ji wani abu cikin zuciyarsa ba. 


"  WADANNAN MANZANNI NE MUN FIFITA SASHENSU AKAN SASHE, DAGA CIKINSU AKWAI WANDA ALLAH YAYI MAGANA DA SHI....... "


             (QUR'AN) 


Yazo cikin (SUNAN AL-MAHASEEN) na Aliyu Bn Abdullah, daga Musa Bn Sa'adaan, daga Abdullahi Bn Qaseem, daga Mufaddal, daga Sadiq, daga babansa (A. S) yace, 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


" LALLE ALLAH YA SANYA ALIYU TUTA ⛳ (ce) A TSAKANINSA DA TSAKANIN HALITTUNSA, BABU WATA TUTA TSAKANINSA DA TSAKANINSU KOMA BAYANSA, DUK WANDA YA BI SHI YA KASANCE MUMINI, KUMA WANDA YAYI JAYAYYA DASHI YA KASANCE KAFIRI, KUMA WANDA YAYI KOKONTO CIKINSA YA KASANCE MUSHIRIKI  ."


سن، المحاسن عَلِيُّ بْنُ عَبْدِ اللَّهِ عَنْ مُوسَى بْنِ سَعْدَانَ عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ الْقَاسِمِ عَنِ الْمُفَضَّلِ عَنِ الصَّادِقِ عَنْ أَبِيهِ ع قَالَ: إِنَّ اللَّهَ عَزَّ وَ جَلَّ جَعَلَ عَلِيّاً عَلَماً بَيْنَهُ وَ بَيْنَ خَلْقِهِ لَيْسَ بَيْنَهُ وَ بَيْنَهُمْ عَلَمٌ غَيْرُهُ فَمَنْ تَبِعَهُ كَانَ مُؤْمِناً وَ مَنْ جَحَدَهُ كَانَ كَافِراً وَ مَنْ شَكَّ فِيهِ كَانَ مُشْرِكاً[29


Yaa Allah ka shaida, mu munyi imani da hakan kuma ba ma jayayya dashi cikin hukuncinKa, sannan ba ma kokonton cewa Kai kake yin komai yadda kaso ba tare da an tuhume Ka ba. 

Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏼Ado Isah Guda. 


      (08126385470)


9th January, 2021/  26th Jimada-Ulah, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post