@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
BA DON ALLAH IBN ABBAS YA YIWA ABUBAKAR MUBAYA'A BA SAI DON GANIN MUTANE SUNYI MASA
Ba kamar yadda wasu ke cewa wai Annabi (S. A. W. W) yayi wasiyyar cewa Abubakar ne Khalifa a bayansa ba , a'a, Ibn Abbas (R. A) ya qaryata wannan magana cikin tattaunawarsa da Imam Ali (A. S).
KU BIYO MU DON GANIN YADDA TA KAYA
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
An karbo daga Ahmad Bn Idrisa, daga Ahmad Bn Muhammad, daga Hassan Bn Abbas Bn Jarishi, daga Abu Ja'afar (A. S) yace : Ameerul-Muminina (A. S) ya fada bayan wafatin Manzon Allah (S. A. W. W) cikin masallaci da sauti madaukaki yayin da mutane suka taru:
أَحْمَدُ بْنُ إِدْرِيسَ، عَنْ أَحْمَدَ بْنِ مُحَمَّدٍ، عَنِ الْحَسَنِ ابْنِ الْعَبَّاسِ بْنِ الْجَرِيشِ[91]، عَنْ أَبِي جَعْفَرٍ عَلَيْهِ السَّلَامُ قَالَ: قَالَ أَمِيرُ الْمُؤْمِنِينَ عَلَيْهِ السَّلَامُ- بَعْدَ وَفَاةِ رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَ آلِهِ فِي الْمَسْجِدِ وَ النَّاسُ مُجْتَمِعُونَ-
بِصَوْتٍ عَالٍ:
" WADANDA SUKA KAFIRTA KUMA SUKA KANGE (mutane) DAGA TAFARKIN ALLAH AYYUKANSU SUN BACI !"
الَّذِينَ كَفَرُوا وَ صَدُّوا عَنْ سَبِيلِ اللَّهِ أَضَلَّ أَعْمالَهُمْ[92].
(سورة محمّد: 1.)
Sai Ibn Abbas (R. A) yace, " Yaa baban Hassan ! Menene yasa ka fadi abinda ka fada ?" Yace,
" WANI ABU NA KARANTA DAGA ALQUR'ANI ." Yace,
" Amma ai ka fada ne don wani al'amari. "
فَقَالَ[93] ابْنُ عَبَّاسٍ: يَا أَبَا الْحَسَنِ لِمَ قُلْتَ مَا قُلْتَ؟! قَالَ: قَرَأْتُ شَيْئاً مِنَ الْقُرْآنِ.
قَالَ: لَقَدْ قُلْتَهُ لِأَمْرٍ؟
Imam Ali (A. S) yace,
" EH HAKANE. LALLE ALLAH (T) NA FADA CIKIN LITTAFINSA, "ABINDA MANZO YAZO MUKU DASHI KU RIQE SHI, KUMA ABINDA YA HANE KU DAGA GARE SHI KU NISANCE SHI ."
" YANZU (kai) KA SHAIDA CEWA MANZON ALLAH (S. A. W. W) YA HALIFANTAR DA ABUBAKAR ?"
قَالَ: نَعَمْ، إِنَّ اللَّهَ يَقُولُ فِي كِتَابِهِ: وَ ما آتاكُمُ الرَّسُولُ فَخُذُوهُ وَ ما نَهاكُمْ عَنْهُ فَانْتَهُوا[94]، فَتَشْهَدُ[95] عَلَى رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَ آلِهِ أَنَّهُ اسْتَخْلَفَ أَبَا بَكْرٍ[96]؟
Ibn Abbas (R. A) yace : " Banji Manzon Allah (S. A. W. W) yayi wasiyya da wani ba face kai ."
قَالَ: مَا سَمِعْتُ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَ آلِهِ أَوْصَى إِلَّا إِلَيْكَ.
Imam Ali (A. S) yace, " TO, (tunda hakane) ME YASA BA KAYI MIN MUBAYA'A BA ?" Yace,
" Mutane ne suka taru akan Abubakar, sai (nima) na kasance daga cikinsu (na bar umarnin Manzon Allah) ."
قَالَ: فَهَلَّا بَايَعْتَنِي؟! قَالَ: اجْتَمَعَ النَّاسُ عَلَى أَبِي بَكْرٍ[97] فَكُنْتُ مِنْهُمْ.
Sai shugaban muminai (A. S) yace: " AI KAMAR YADDA MUTANEN 'DAN MARAQI NE SUKA TARU AKAN 'DAN MARAQI, KAMAR HAKA AKA FUTINE KU . " MISALINKU SHINE KAMAR MISALIN WANDA YA KUNNA WUTA , YAYIN (da hasken) YA HASKAKA ABINDA KE KEWAYE DASHI (na tsoro) SAI ALLAH YA TAFIYAR DA HASKEN NASA, KUMA YA BARSU CIKIN DUHU BA SA GANI. (suka kasance) KURAME BEBAYE MAKAFI, KUMA SU BA ZA SU (taba) DAWOWA (kan hanyar gaskiya) BA ."
فَقَالَ أَمِيرُ الْمُؤْمِنِينَ عَلَيْهِ السَّلَامُ: كَمَا اجْتَمَعَ أَهْلُ الْعِجْلِ عَلَى الْعِجْلِ، هَاهُنَا فُتِنْتُمْ، وَ مَثَلُكُمْ كَمَثَلِ الَّذِي اسْتَوْقَدَ ناراً فَلَمَّا أَضاءَتْ ما حَوْلَهُ ذَهَبَ اللَّهُ بِنُورِهِمْ وَ تَرَكَهُمْ فِي ظُلُماتٍ لا يُبْصِرُونَ صُمٌّ بُكْمٌ عُمْيٌ فَهُمْ لا يَرْجِعُونَ[98].
تفسير القمّيّ 2- 301.
(7) في المصدر: الحريش.
بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج29، ص: 20
Subhanal-Lah, amma duk da wannan hujja ta yakan hanzari daya ba shi amma bai canza daga kan bin abinda mutanen suka zaba ba, haka ma sauran mutanen dake gurin suna saurare basu bi wannan gaskiyar ba.
Ko da shike maganar Allah ce ta tabbata cewa sun kurmance (daga jin gaskiya) kuma sun bebance (yadda ba za su iya yiwa junansu gargadi da nasiha ba), kuma sun kurmance (daga jin gaskiya yadda ko sun ji ta ba za su fahinceta ba ballantana suyi aiki da ita).
YAA ALLAH KA TABBATAR DAMU KAN GASKIYA.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.
(08137925034)
10th January, 2021/ 27th Jimada-Ulah, 1442.