@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
DA A BA KA ADDINI GARA A BA KA HANKALI
Kunya na daga cikin kyawawan dabi'u kuma siffa ta Annabawa (A. S) wacce ake fatan kowa ya siffantu da ita, haka ma riqo da addini siffa ce wacce ke nuna cewa mutum na kirki ne, sai dai dukkan su ba sukai hankali a matsayi wajen Allah ba.
Wannan na daga cikin dalilin da yasa a ko da yaushe shari'ar muslimci na tafiya ne tare da hankali.
Domin samun gamsuwa da wannan magana tawa ku biyo mu cikin wannan rubutu da ke biye.
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
Ya zo cikin Al-Khisaal na Amali Lis-Sudduq Bn Barqeey, daga babansa, daga kakansa, daga Amru Bn Usman, daga baban Jamilata, daga Ibn 'Darif, daga Ibn Nubatata, daga Aliyu Bn Abiy 'Dalib (A. S) yace,
الخصال لي، الأمالي للصدوق ابْنُ الْبَرْقِيِّ عَنْ أَبِيهِ عَنْ جَدِّهِ عَنْ عَمْرِو بْنِ عُثْمَانَ عَنْ أَبِي جَمِيلَةَ عَنِ ابْنِ طَرِيفٍ عَنِ ابْنِ نُبَاتَةَ عَنْ عَلِيِّ بْنِ أَبِي طَالِبٍ ع قَالَ:
" Jabra'ilu (A. S) ya sauko zuwa ga Adamu (A. S), sai yace, " YAA ADAMU ! LALLE NI AN UMARCE NI DANA ZABA MAKA (abu) 'DAYA CIKIN UKU, (saboda haka) KA ZABI 'DAYA KA BAR BIYUN ." Sai Adam (A. S) yace masa,
" Menene abu ukun nan yaa Jabra'ilu ?" Sai yace masa;
(1)- HANKALI, da
(2)- KUNYA, da
(3)- ADDINI.
Sai Adam (A. S) yace, " To, ni na zabi hankali ."
Sai Jabra'ilu (A. S) ya cewa kunya da addini,
" KU TAFI !"
Sai suka kira shi suka ce, " Yaa Jabra'ilu ! Lalle mu an umarce mu da muke kasance tare da hankali a duk inda yake ."
Sai (Jabra'ilu) yace, " KUYI AIKIN KU, KUMA KU BIJIRO (ku zo) ."
هَبَطَ جَبْرَئِيلُ عَلَى آدَمَ ع فَقَالَ يَا آدَمُ إِنِّي أُمِرْتُ أَنْ أُخَيِّرَكَ وَاحِدَةً مِنْ ثَلَاثٍ فَاخْتَرْ وَاحِدَةً وَ دَعِ اثْنَتَيْنِ فَقَالَ لَهُ آدَمُ وَ مَا الثَّلَاثُ يَا جَبْرَئِيلُ فَقَالَ الْعَقْلُ وَ الْحَيَاءُ وَ الدِّينُ قَالَ آدَمُ فَإِنِّي قَدِ اخْتَرْتُ الْعَقْلَ فَقَالَ جَبْرَئِيلُ لِلْحَيَاءِ وَ الدِّينِ انْصَرِفَا وَ دَعَاهُ فَقَالا لَهُ يَا جَبْرَئِيلُ إِنَّا أُمِرْنَا أَنْ نَكُونَ مَعَ الْعَقْلِ حَيْثُمَا كَانَ قَالَ فَشَأْنَكُمَا وَ عَرَجَ.
بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج1، ص: 87
NAZARI
-------------------
Idan mu kayi nazari da hankalin da Allah ya bamu kuma yace mu riqa yin tunani da shi wajen tantance gaskiya da qarya, ko mummuna daga kyakkyawa , za muga cewa akwai yanayi dake kasancewa yadda kunya da addini za su iya gushewa tare da mutum.
Idan ba ku fahinci hakan ba sai nace muku, ya kuke gani game da wanda ya sami tabin hankali (hauka), akwai kunya da addini tare da shi ?
Shi kuwa mutumin da Allah ya ba shi hankali za ka tarar da kunya da addini na tare da shi cikin komai nasa ! Idan kuwa kaga bamu ba shi da addini ko kunya tare da shi, to, ka kira shi Mahaukaci, domin mai hankali ba zai taba yiwuwa ya nisanci aiki da addininsa ba, kuma ba za kaga yana aikata abubuwa na rashin kunya ba, domin ya san ana samunsu ne wajen mai rabon lahira.
Saboda haka a duk lokacin da aka ce ka rasa hankali, to, ka rasa komai naka na alkhairi.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.
(08137925034)
7th January, 2021/ 24th Jimada-Ulah, 1442.