Kukan kurciya: Halina a matsayin dan gwagwarmaya

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @



        KUKAN KURCIYA 


To, yau nayi nufin bayyanar muku irin halina ne, a gwagwarmaya  bana bada yin infaƙi (Taimako) kamar yadda ya kamata ace ina yi a matsayin na dan gwagwarmaya.  Ni kaina ina zargin kaina, kuma idan akwai mai irin wannan hali nana ya daina ko ya gyara kar na zama abin koyi gare shi. 


Na kasance a duk lokacin da aka nemi infaƙi na ɗari biyar (500) a gurina   kacal ba na iya bayarwa sai na dinga karanto  matsalolin dubu 20,000. ne a gabana .


Abinda yafi damuna da irin wannan halin nawa shine, ba na iya bada Infaƙin amma a kullum idan naga abin duniya wanda ya burgeni yanzu zanje na sayo shi komai tsadarsa, kai  harma bashi  (loan) nake nema idan kudina bai cika ba.


Ni ɗan gwagwarmaya ne amma har  yanzu na kasa gane ne kaina akan wannan al'amarin. Matsalar tawa har yau din nan a duniya sunke ƙare min, kuma gashi dai  naƙi bada Infaƙi.


Yanzu zan iya ganin  babbar waya ko kuma mashin ko dai computer domin jin dadin rayuwata, sannan komai yawan kudinsu  zan nemo na saya don ina da hanya, kuma na  na riƙe su a hannuna bani da wata damuwa. 


Wayyoh  Allah ni 'Dan Gwagwarmaya😭 !


 Ɗan'uwa, idan aka zo  bangaren  taimakon haƙƙin Shuhada'u sai ka tausayamin domin takaici.  Ni dai ban taɓa sauke #1,200 na haƙƙin Shuhada'u da yake kaina  ba 😭😭😭, kuma a hakan nake kaunar inyi Shahada.


Mai karatu !  Idan na cigaba da rubuta maka halayena a matsayina na  Ɗan gwagwarmaya baza ka ji dadi ba, hasalima kuka ne kawai za ka tayani...


'Yan'uwa ku tayani da addu'arku kawai yanzu akan wannan hali nawa.


YAA ALLAH KA YAQI ZUCIYATA DA ZUCIYAR MASU HALI IRIN NAWA. 


~ Abubakar Aliyu Ahmad Ningi. 


11th January, 2021.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post