Tabbas Imam Ali Alaihissalam yazamo wata aya wadda zamu iya gane Addinin Muslunci dashi cewar shine Addinin gaskia da Hakika.
Tabbas ana iya gane tafarkin gaskiya da magabatan wannan tafarki, meyasa ayau kafirai da Mulhidai suke aibata muslunci da musulmai?
Amsa itace.
Ayau Addinin muslunci duniya tana hukunta shi da wasu mutane wadanda suka kwaci ragamar musuluncin takarfin tsiya suka nada kansa tun bayan Shahadar Manzan Allah s.a.w.w sun dora kansu bada Umarnin Allah ba ballantana Manzan Allah, suka akaita abinda suka akaita.
Agefe guda kuma ga wanda Allah da Manzansa sukayi Umarnin ayiwa da'a da biyayya bayan wafatin Manzan Allah s.a.w.w amma suka ki, sukabi son ransu.
Hakan yasa abubuwa suka faru wanda yajanyo lalacewar jagorancin Addinin Muslunci tun ajiya har zuwa yau saboda Kinbawa masu hakki hakkinsu.
Idan sun tashi fadar wani abu akan muslunci sai sukalli wadannan mutane su hukunta Addini dasu.
Amma tabbas duk wanda yakalli Imam Ali Alaihissalam kuma yakaranci Sirarsa to babu makawa bazai tabayin wani Addini ba face Addinin da Imam Ali Alaihissalam yayi wafati akansa, saboda Imam yana daya daga cikin ayoyin Ubangiji wanda suke nuna cewar hanyarsa itace hanya guda daya madai dai ciya tasamun tsira duniya da Lahira.
Kuma da ace duk wani wanda zai hukunta Addinin Islama yana kallon wannan babban bawa bayan Wafatin Manzan Rahma Alaihissalam, Wato Imam Ali zaiga cewar shine mai bawa halitta dukanta yanci da tausayi ga Mata dajin kan marayu da tallafawa masu rauni da Insaniyya cikakkiya.
Amma ina😭😭
Sai suka zalunci wannan babban bawa na Allah suka kashe matarsa suka kashe shi, suka kashe yayansa suka hana asaurareshi suka hana afadi irin gudun mawarda yabawa Muslunci suka biya kudi aka dinga zaginsa, suka saki Dinare da zahab aka dinga yimasa karya😭😭
Wannan shine yasanya Musulunci da musulmai halinda suke ciki ayau.