Kalamai sunada matukar tasiri a ruhin yaro, sau da dama zayaji wasu kalaman da bai dace ace yajisu ba, kuma suyiwa rayuwarsa tasiri sosan gaske.
Iyaye mata dama maza gaba daya, yanada kyau mu rika sanin abinda zamu fada agaban yara, domin mu muna daukar ma'anar kalmami daban dasu ne, zamu fadi wani abun da irin tamu ma'anar, bayan a wurin yaro shi hankalinsa baikai na ya fahinta abinda ake nufi dinba. Sannan komi kukayi ku iyayensa to kawai yana ganin shine daidai.
Kalamai nayin tasiri sosai ga yara, kuma musamman ma marasa Dadi, ga yarinya mace kalaman zagi ko yabon miji suna saurin tasirantarta ne, kuma zasu kai har lokacin aurenta.
A matsayinki na uwa mahaifiya bai kamata ace kowane kalma kina fadawa mijinki gaban yara ba, saboda suna koyane, idan ya zamana idan kuka samu sabani a gaban yaran kuke maganar, to tabbas wata rana zakiji tana kokarin yin irin makamancin abinda kikayi din, wasu iyayen nada dabi'ar zagi a gaban yara wanda samun tabbacin zaya koyane a bayyane yake, meyasa ake gudun yaro ya rika fita wurin yara barkatai, saboda kar yaje ya jiyo koya koyo wasu ababen da basu dace ba.
Amma dayawan iyaye muna tufka muna warwara mukeyi, sai ki hana yaro fita saboda karya dauko dabi'un banza, ke kuma naki suna masa tasiri.
Dayawa bama gane illar hakan musamman a wurin yara mata, sai idan tayi hankalin sannan koma anyi mata aure sannan tasirin hakan zaya bayyana gareta.
Dabi'a naso takeyi, idan kina yawan aikata abu mai kyau ne ko mara kyau, to tabbas wata rana bama saikin fadawa yaro ba zakiga yanayi da kansa, kamar misalin sallah ne ga yara " akwai wata mahaifiya da takeda da yaro namiji karami, ta kasance duk sanda zatayi sallah sai tace masa yayi alwala yazo suyi sallah, bayan wani dan lokaci ya rigada ya tasirantu da hakan, harya fara dan girma amma saboda mahaifiyarsa yaga da hijab take sallah sai yake tunanin to kowama dashi yakeyi, duk sanda zayayi sallah saiya dauka hijab din mamansa ya saka sannan" kunga kenan da ace wannan mahaifiyar dabi'ar zama taji waka gareta, to Tabbas wata rana zata tsinci yaronta da MP yanajin waka, saboda yaro a wurinsa komi dai_dai ne, kece zaki rika nuna masa rashin dacewar abu da kuma dacewar sa.....
Zan cigaba insha Allah
✍️ Zarah A Zamsarf