Gwamnatin Da Ke Tsare Da Shaikh Zakzaky Ita Ke Kashe-kashen Mutane!



Babu ko shakka cewa daga dalilan da yasa gwamnatin Buhari ke cigaba da tsare Shaikh Zakzaky a tsawon shekaru biyar din nan duk da umurnin kotu kan a sake shi amma sun ki sakinsa, akwai bukatar da suke da shi na samun damar cigaba da kai hare hare da kashe mutane da sunan yan ta'adda a dukkan sassan Kasar nan.


Tun kan Boko Haram, Shaikh Zakzaky ne malami daya tal a duk fadin kasar nan da ya nunawa gwamnati yatsa tun a 2009 kan cewa karyar banza ce diramar Boko Haram, kawai kokarin wasa da addinin Musulunci ne ta hanyar Ta'addanci da sunansa, da kuma kokarin Amurka don wargaza kasa da cigaba da kai hare-hare don daga baya ta zo tace za ta kawo tsaro a kasar ta rika diban albarkatun karkashin kasa.


A 2013 da 2014, Shaikh Zakzaky yayi bayani mai gamsarwa a kan shirin Turawa da hadin guiwar gwamnatin kasar nan na dira a kan al'ummar yankin Katsina, Zamfara, Sokoto da Birnin Gwari/Kaduna, don su tarwatsa kowa daga yankin, ya zama ba kowa wajen ya zama falalen da mutane ba su rayuwa sai su gina sansanoninsu su rika diban albarkatun yankin suna fita da su.


Video din bai buyawa yan Nijeriya ba har yanzu akwai shi a YouTube, kuma duk abin da yake fada din a lokacin shine yake faruwa a yanzu haka da gwamnati ke tsare da shi. Mai so ya kalli Video din a nan https://youtu.be/pULPogqdURk


Da ace Shaikh Zakzaky na waje, shi kadai ne malamin da Allah Ya ma baiwar gano gaskiyar al'amari kai tsaye kuma ya fade shi a yadda yake, wanda wannan fadan da yake ba karamin tonawa masu mugun kullin asiri yake ba, har ya zama sun fasa ko kuma shirinsu ya rushe ya zama bai yi tasirin da ake tsammani ba.


Amma da cigaba da tsare shi da suke yi, an rasa wani tsayayye kamar sa in ba a almajiransa ba, wanda al'umma suke saurarawa, kuma maganarsa ke iya zama wa hukumar da ita ke kashe mutane alakakai! Ba wata tantama gwamnati da Jami'an tsaronta ke Ta'addanci ko da akwai wasu mutane daban yan Ta'adda, to kawai suna taya gwamnati cimma muradi uwar gijiyarta, Amurka ne. Wacce bama wani tantama cewa har da wannan dalilin a cikin dalilin rike Shaikh Zakzaky bisa zalunci a kurkuku!

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post