BISMILLAHI-RAHMANUR-RAHIM
A tsawan zamani mace ta kasance abar da ake jinginama kalmar rauni a kowace al’umma, ta inda ake mata kallon bazata iya komaiba face kula da yara, girki da ayyukan gida. Akan tauye mata hakkin neman ilimi ko kuma bada wata gudunmawa don cigabantar da al-ummarta, akan maida ita tamkar baiwa.
A mahangar addinin Musulunci mace tanada kima sosai, sannan kuma tanada cikakken ‘yancin yin duk wani abu matukar zata kiyaye sharudda da koyarwar addini. Kama daga kasuwanci, fafutukar neman ‘yanci, neman ilimi da sauransu. Tana da cikakkiyar damar hulda da al-umma datake rayuwa dasu matukar zata kiyaye shari’oin addininta. Amma duk da wadannan damarmaki da yanci da musulunci ya bata be hana al-umma cigaba da tauye mata hakkinta ba wanda kai tsaye ya sabama koyarwar addinin musulunci.
Duk da wannan yanayi da mata suke samun kansu, tarihi ya nakalto jaruman mata dadama wadanda suka bada gudunmawa wurin cigabantar da al-ummarsu a fannin addini, ilimi, siyasa d.s. Misali Sayyida Hannah mahaifiyar Sayyida Maryam (AS), ta jajirce wajen sadaukar da jaririyar ‘yarta zuwa ga hidimtawa addinin Allah (SWT). Haka ita kanta Sayyida Maryam din tayi gwagwarmayan tasowa tsakanin yahudawan zamaninta kuma ta fuskancesu ba tare da tsoro ba. A lokaci guda kuma tana hidimtawa addinin Allah har karshen rayuwarta.
Haka kuma idan mukai duba ga Sayyida Asiya (AS) matar Fir’auna (L), duk da kasancewarta matar azzalimin sarki, be hanata yin gwagwarmayar tsayuwa da dakewa akan gaskiya ba. Dukda ukuba da azabar data fuskanta daga mijinta, har ta samu tsira.
Sannan idan mukai duba a wannan zamanin na Manzon tsira (SAWW) zamuga akwai mata irinsu Sayyida Khadija (AS) wacce ta sadaukar da dukkan dukiyarta data mallaka ga addinin Musulunci. Ga kuma ‘yarta shugaban matan duniya, itama ta sadaukar wajen kariya ga Manzon Allah (SAWW) a duk lokacin da mushrikai suka farmasa, sannan ta tsaya kyam a gefen Imam Ali (AS). Sayyida Zainab (AS) itama tayi gwagwarmaya tun daga yarintarta har ta koma ga mahaliccinta. Haka kuma a Karbala akwai mata dayawa da suka sadaukar irinsu Dilham matar Zuhair wacce ta karfafi mijinta akan ya shiga filin daga, da Atika matar Wahab Bn Abdallah wacce ta sadaukar da mijinta da Rubab da kuma Ummu Wahab amincin Allah ya tabbata a garesu.
A wannan zamanin namu akwai su Amina As-sadar (Bintul Huda), wadda Sadam ya kasheta tare da dan’uwanta. Akawai Jannah Tamimi (Youngest journalist) data fara aikin media tin tana yar shekara 7, tana yada zaluncin da ake a kasarsu ta Palestine. Sannan ga Umma Zeenat (Allah ya kara mata lafiya) wacce ta sadaukar da ‘ya’yanta 6 don daukaka karmar Allah, kuma ta kasance mana madubi a gwagwarmaya.
Idan mukai duba a rayuwar wadannan jaruman bayin Allah zamuga sun bada babbar gudunmawa don daukaka adalci da fada da zalunci, kuma muma lokaci bai kure manaba zamu iya bawa addini gudunmawa fiye da tinanin me tinani, matukar zamu shirya kanmu mu sauke nauyin dake kanmu mukuma dogara ga Allah (SWT).
A karshe ina me tinatar damu cewa aduk inda Allah (SWT) yace muminai maza zaice muminai mata, sannan yana cewa ‘babu wanda yafi wani a gurin Allah sai wanda yafi tsoranshi’.