@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
KASANCE CIKIN MASU ZIKIRI BAYAN SALLAH
Kalmar ziriki tana nufin ambaton Allah ta kowacce fuska, za ta iya kasancewa a bayyane ko a boye.
Kuma cikin kowanne irin hali za ka iya yi, wato a tsaye ne ko a zaune ko kuma a kishingide.
A wata fassarar kuma sallah ko karatun Alqur'ani ma kan iya zama zikiri, domin duk wani abinda za kayi wanda za ka tuna da Allah ko ambatonsa, to, wannan zikiri ne.
Ya zo cikin Tafsirul-Ayaashiy Abu Hamzatal Thumaaliy, daga Abu Ja'afar (A. S) yace,
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
" MUMINI BA ZAI GUSHE BA YANA CIKIN SALLAH MATUQAR YA KASANCE YANA AMBATON ALLAH (zikiri). KO DA YA KASANCE A TSAYE NE KO A ZAUNE KO KUMA A KISHINGIDE, DOMIN ALLAH (T) NA CEWA; " SUNE WADANDA KE AMBATON ALLAH A TSAYE DA ZAUNE DA KUMA AKAN BANGARENSU (kishingide) ."
34- شي، تفسير العياشي أَبُو حَمْزَةَ الثُّمَالِيُّ عَنْ أَبِي جَعْفَرٍ ع قَالَ: لَا يَزَالُ الْمُؤْمِنُ فِي صَلَاةٍ مَا كَانَ فِي ذِكْرِ اللَّهِ إِنْ كَانَ قَائِماً أَوْ جَالِساً أَوْ مُضْطَجِعاً لِأَنَّ اللَّهَ يَقُولُ- الَّذِينَ يَذْكُرُونَ اللَّهَ قِياماً وَ قُعُوداً وَ عَلى جُنُوبِهِمْ[70] الْآيَةَ.
Saboda haka ba qaramin kuskure bane ko hasara ace mutum yayi sallah ba zai tsaya yayi zikirin Allah ba, domin dukkanmu masu gazawa ne sannan masu aikata sabo ne, saboda haka ya kamata mu riqa kasancewa masu tsayuwa muna ambaton Allah don neman gafararsa da samun yardarsa .
Allah (T) na cewa ,
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
" IDAN KUKA QARE (idar da sallah) KU KAFU (kuma masu qasqantar da kanku) .
KUMA ZUWA GA UBANGIJINKA KA KWADAITU (wajen neman gafararsa da biyan buqatu daga gare Shi) ."
فَإِذَا فَرَغۡتَ فَٱنصَبۡ ٧ وَإِلَىٰ رَبِّكَ فَٱرۡغَب ٨
(SURATUL-SHARHI :7-8)
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.
(08126385470)
3th January 2021/ 20th Jimada-Ulah, 1442.