Duk Brother ko Sister da Suke Fira Awajen Program Wallahi basu Biyayyah ga Maganar Sayyeed Zakzaky (H)...!!!



Akwai wata rana a Hussainiyyah baqiyatullah Ranar 1 ga watan Ashura sayyeed yana Magana akan Halayyar wasu 'Yan uwa Awajen Program to anan sai yake cewa..

"Malama Zeenat ta fa'damin Wata rana a Hussainiyyah ta shiga 'Daki haka, sai taji wani brother yana cewa da wata sister kedai kawai kicee baki SONA!


Sai Malama tayi 'Kokarin fitowa taga su wanene,

Sai take cewa ina ganin motsina sukaji suka ruga amma tabbas naso ganinsu, Alhalin Sayyeed nacan yana Jawabi.


To anan Sayyeed yake cewa wajen Program ba wajen neman Aure bane, Idan mutum zai nemi aure kamata yayi, yaje gidan su, ya nemi izinin Mahaifan ta.


Note: Ya kamata 'Yan uwa Brothers & Sisters musan me muke idan muka zo wajen Program to ya kamata mu bada lokacin mu, domin sauraron me za'a fadi.


Kaga wadannan 'yan uwan sun nuna a fili sharholiyarsu tafi sauraron jawabin jagora!


Elahy ya bamu ikon biyayyah ga maganar jagora.


 --Aljawad Jibrin Kagara (Dan jaridah)

 --09/01/2021

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post