Yayin yake ƙarin bayani kan wannan wajen wanda gidan talabijin ɗin ƙasar ya nuna shi, Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci Manjo Janar Hossein Salami ya bayyana cewar sansanin dai ɗaya ne daga cikin sansanonin da sojojin ruwa na dakarun kare juyin Musulunci suke ajiye da makamansu masu linzami.
Janar Salami ya ce makamai masu linzamin da aka jibge su a wajen suna cin zango na ɗaruruwan kilomitoci ne kuma suna da ƙarfi tarwatsa duk wani wajen da ake so su tarwatsa kamar yadda kuma suna iya tsira daga ganowa ko kuma tarwatsawar makaman maƙiya.
Kalli Bidiyon Anan:
Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci ya kara da cewa makamai masu linzamin da sojojin ruwa na dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran suka mallaka suna daga cikin makamai masu linazami na zamani kuma masu karfin gaske da za a iya amfani da su daga doron kasa zuwa cikin teku, sannan daga teku zuwa teku, daga doron ƙasa zuwa doron ƙasa sannan daga sama zuwa teku.
Janar Salami ya ci gaba da cewa a duk lokacin da buƙatar amfani da waɗannan makamai ta taso Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba za ta yi ƙasa a gwuiwa wajen kare kanta ba.
A shekarar da ta gabata ce dakarun kare juyin juya halin Musuluncin suka sanar da ƙera wani ‘birnin makamai masu linzami’ suna masu jan kunne maƙiya da kada su bari wani gigi ya ɗebe su su kawo wa ƙasar hari.
Majiya: Abna24.com