@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
Hanyar neman arziqi hanya biyu ce, ta hanyar halal da kuma haram, kuma akan same shi ta kowacce irin hanya.
Cikin wadannan hanyoyi biyu manya kuwa akwai wasu abubuwan da mutum kan aikata kafin fadawa kan wadannan hanyoyi. Aikin qarfi ne ko na ilimi ko kuma wasu dabaru wadanda mutun zai iya tsiwirwirta don samun wani abu da zai biya buqatunsa.
Ibn Abbas (R. A) ya fada cikin wa'azozinsa cewa,
قال ابن عباس رضي الله عنهما:
" BABU WANI DAGA MUMINI KO FAJIRI FACE ALLAH YA RUBUTA MASA (hanyar samun) ARZIQINSA DAGA HALAL. IDAN YAYI HAQURI HAR YAZO MASA, TO, ALLAH ZAI ZO MASA DASHI . IDAN KUWA YA GAGGAUTA YA NEME WANI ABU DAGA HARAM, TO, ALLAH ZAI TAUYE MASA DAGA ARZIQINSA NA HALAL ."
" ما من مؤمن ولا فاجر إلا وقد كتب الله تعالى له رزقه من الحلال، فإن صبر حتى يأتيه، آتاه الله تعالى، وإن جزع فتناول شيئًا من الحرام، نقصه الله من رزقه الحلال. "
(MAWA'IZUS-SAHABAH)
Saboda haka fajiri zai iya tara arziqi ta hanyar matuqar ya bi ta hanyarta, haka kuma musulmi zai iya tara arziqin haram in ya bi ta hanyarta.
MU TSARKAKE HANYOYIN SAMUN ARZIQINMU.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.
(08137925034)
4th January, 2021/ 21st Jimada-Ulah, 1442.