Cutar zuciya tafi ta corona virus illa

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED  @




TALAUCI SHI YAFI KOMAI SAUQI DAGA CIKIN CUTUTTUKA 


Sakamakon juyawa tsarin Allah baya ya sanya al'umma fadawa cikin musifu, qunci da kuma fuskantar cututtuka masu wuyar magancewa kuma masu saurin yaduwa cikin duniya.


Talauci na daga cikin ciwon da aka fi fuskanta a baya, domin a wancan lokaci babu yawan cututtuka, kuma ko da ace mutum ya kamu da rashin lafiya cikin sauqi yake warkewa ba tare da hasarar dukiya ba, amma  cutar yanzu sai kaji ana kiran #1,000,000 (1 m) a matsayin abinda za a kashe kafin samun lafiya,  kaga idan irin wannan cuta ta sami talaka sai dai ya mutu. 


Wannan na nuna mana ne cewa ashe talauci ciwo ne, sai dai kuma duk da irin wannan matsayi nasa rashin lafiyar zuciya ya fi shi muni. 


DAGA IMAM ALI (A. S) 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


وَ أَرْوِي أَنَّ أَمِيرَ الْمُؤْمِنِينَ ع قَالَ فِي كَلَامٍ لَهُ‏ إِنَّ مِنَ الْبَلَاءِ الْفَاقَةَ وَ أَشَدُّ مِنَ الْفَاقَةِ مَرَضُ الْبَدَنِ وَ أَشَدُّ مِنْ مَرَضِ الْبَدَنِ مَرَضُ الْقَلْبِ


An riwaito cewa shugaban muminai (Imam Ali (A. S)) ya fada cikin kalamansa cewa, 


" LALLE TALAUCI NA DAGA CIKIN BALA'I , KUMA ABINDA YAFI TALAUCI TSANANI SHINE CIWON GANGAR JIKI, KUMA ABINDA YAFI TSANANI DAGA CUTAR GANGAR JIKI SHINE CUTAR ZUCIYA  ."


NB:-


Ita wannan cuta ta zuciya ba ana nufin irin cutar da ake tafiya asibiti  ko shan maganin gargajiya don magancewa shi bane, a'a, cuta ce ta kafirci ko munafurci ko kuma ta goyawa kafirci baya da hada kai ta kowacce fuska don yaqar muslimci da ma'abotarsa. 




Saboda haka duk wanda ya kamu da irin wannan cuta babu maganin duniya ko kudin da zai iya magance shi in ba mutum ya tsarkake zuciyar tasa ba. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏼Ado Isah Guda. 


         (08137925034)


9th January, 2021/ 26th Jimada-Ulah, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post