Wa'iyazubillah yanzu muna wani yanayi wanda Zinace-zinace ya yawaita acikin Al'ummah ba Dattawa da samari.
Wanda kullum kara samun gurbin zama take a zukatan jama'a musamman matasa majiya karfi.
Cikin wannan Yanayin da ake ciki wasu daga cikin 'yan uwa suma suka 'dauki dabi'ar Aikata wannan mummunan aiki wai a matsayin mafita agaresu sakamakon Tsa'dar Ku'din aure ga kuma yanayi na tsadar rayuwa da ake cikii.
Ko Yaushe mabiyin sayyeed ya zamto mai karamin tunani?
Ko yaushe mai Ikirarin shi mabiyin sayyeed ne, ya zamto zuciyar shi ce mai sarrafa tunanin shi?
MAFITA....
Yin black market a tsakanin mu, bazai kawo mafita wlh.
Dole mu ha'du karfi da karfe domin kawar da wannan 6arakar.
Ni a tunani dole ya zamto mun samu fahimtar juna tsakanin mu da iyayen 'yan mata.
Dole kai a matsayinka na Uba kaji cewa zaka iyayin komai domin kare yarka daga shiga halaka, kada kayi duba dame saurayin da, zai auri 'yarka ya kawo a matayin dukiyar aure, A A kayi duba da cewa wannan hanyar ce, ta ku6utar da 'yarka daga fadawa halaka.
Kai kuma saurayi kada kayi duba da ku'din da aka yanka maka wanda zaka biyaa A A kayi duba da Darajar ta, sannan ka dauketa a matsayin Kanwarka wacce zaka iyayin komai domin kare mutuncin ta, domin kome ka biya wlh basu kai darajar taba.
Iyaye ku Saukaka ku'di, ku kuma samari kuyi kokarin yin abinda ya dace domin mu rufawa junan mu asiriii fakat! 🙅🏿♂️
--Aljawadu jibrin kagara (Dan jaridah)
--10/01/2021