Gwamnan Jihar Neja da ke arewacin Najeriya, Abubakar Sani Bello, ya ce ba zai yi ko wacce irin sasantawa ba da 'yan bindigar da suke 'ta'addanci' ba a jihar.
Gwamna Bello ya yi wannan kalamai ne lokain da yake amsa tambayoyin manema labarai bayan kammala wata tattaunawa da ya yi da shugaban ƙasar Muhammadu Buhari a fadar shugaban da ke Abuja, game da ƙaruwar matsalar rashin tsaro da kuma lalacewar ababan more rayuwa a jihar.
Gwamnan ya ce ya dakatar da duk wata dama ta tattaunawa da waɗannan 'yan bindiga, saboda ba sa tsayawa kan alƙawarinsu, domin a baya ya taɓa yin irin wannan yarjejeniya da su kuma ba ta kawo wani sauyi ba.
Bello, ya ce a kwanan nan jihar na fuskantar tururuwar 'yan bindiga waɗanda suke shiga ta kan iyakar Jamhuriyar Benin, yana mai cewa " Fulani ne waɗanda ba su da mai fada musu su ji ko da iyayensu ne."
Ya kuma ce matsalar 'yan bindiga ita ce ta fi damun gwamnatin jihar a yanzu.
Ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa ta kama wasu dagattai sakamakon zargin su da haɗa kai da ƴan bindiga domin aiwatar da hare-hare.
Source: Niger State Media 24News