@MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
ILLOLIN KWADAYI, GIRMAN KAI DA KUMA HASSADA
Idan kaji an ambaci kalmar kafirci a haqiqanin ma'anarta shine qin gaskiya da guje mata, ba wai ana nufin barin muslimci bane. Shi yasa ake samun kafirai cikin musulmai, wato wadanda suka ga gaskiya amma suka qi binta don bin son zuciyarsu.
Allah (T) na cewa,
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
" ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ وَصَدُّواْ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِ أَضَلَّ أَعۡمَٰلَهُمۡ .( ١ )
" WADANDA SUKA KAFIRTA KUMA SUKA KANGE (mutane daga bin h) HANYAR ALLAH AYYUKANSU SUN BACI ."
(MUHAMMAD :1)
Kunga wannan ayar ba tana magana ne akan kafirai ba, a'a, tana magana ne kan musulmai wadanda suka juya baya daga bin umarnin Manzo Allah (tsira da aminci su tabbata a gare shi), domin su kafirai (wadanda ba musulmi ba) ba su da wani aikin lada wajen Allah ballantana ma ace ya baci saboda wani aiki da suka aikata daga baya.
Abu Abdullah (A. S) ya nuna mana ko yi mana bayani game da asalin kafirci cewa abubuwa uku ne, sai ku biyo mu don ji da gani cikin nassin hadisin.
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
الكافي الْحُسَيْنُ بْنُ مُحَمَّدٍ عَنْ أَحْمَدَ بْنِ إِسْحَاقَ عَنْ بَكْرِ بْنِ مُحَمَّدٍ عَنْ أَبِي بَصِيرٍ قَالَ قَالَ أَبُو عَبْدِ اللَّهِ ع أُصُولُ الْكُفْرِ ثَلَاثَةٌ الْحِرْصُ وَ الِاسْتِكْبَارُ وَ الْحَسَدُ فَأَمَّا الْحِرْصُ فَإِنَّ آدَمَ ع حِينَ نُهِيَ عَنِ الشَّجَرَةِ حَمَلَهُ الْحِرْصُ عَلَى أَنْ أَكَلَ مِنْهَا وَ أَمَّا الِاسْتِكْبَارُ فَإِبْلِيسُ حِينَ أُمِرَ بِالسُّجُودِ لِآدَمَ اسْتَكْبَرَ وَ أَمَّا الْحَسَدُ فَابْنَا آدَمَ حَيْثُ قَتَلَ أَحَدُهُمَا صَاحِبَهُ[1].
(1) الكافي ج 2 ص 289.
Yazo cikin Kafiy, daga Hussaini Bn Muhammad, daga Ahmad Bn Ishaq, daga Barin Bn Muhammad, daga baban Basheer yace, Abu Abdullah (aminci ya tabbata a gare shi) yace;
" ASALIN KAFIRCI (abu) UKU NE,
- KWADAYI,
- DA GIRMAN KAI, DA KUMA
- HASSADA.
AMMA KWADAYI, ABIN SANI YAYIN DA AKA HANI ADAM DAGA (cin 'ya'yanmu) ITACIYA KWADAYI NE YA 'DAUKE SHI ZUWA CI DAGA GARE TA (saboda jin abinda Shaidan (L. A) ya fada masa cewa matuqar ya ci 'ya'yan wannan itaciya zai dawwama cikin aljannah da kuma mulki wanda bai qarewa).
AMMA KUMA GIRMAN KAI, SHINE IBLIS YAYIN DA AKA UMARCE SHI DA YIN SUJADAH GA ADAM SAI YAYI GIRMAN KAI.
ITA KUWA HASSADA, ITA CE NA 'YA'YAN ADAM YAYIN DA 'DAYANSU YA KASHE 'DAN'UWANSA ."
Anan za muga cewa wadannan abubuwa uku sune asalin kafirci, domin duk wani abinda zai yi sanadin kangarewa Allah yana qarqashinsu ne.
YAA ALLAH KA KIYASHE MU DAGA WADANNAN KAFIRCI 🙏🏿🙏🏿🙏🏿
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.
(08137925034)
13th January, 2021/ 30th Jimada-Ulah, 1442.