Daga Ma'asumah Nigerian News Update.
A cikin jawabin Malam Kasim Shinkafi na rufe mu'utamar din da shafin Ma'asumah ta shirya ga wakilanta, wanda ya gudana a ranakun 1,2 da 3 ga watan Junairun 2021 a garin Shinkafi ta Jahar Zamfara. A cikin jawabin nasa Malam Yayi kira da masu ta'ammuli da yanar gizo wajan isar da sako da suyi kokarin kyautata rubutunsu ta hanyar bin kowace ka'ida da doka ta rubutu a cikin kowane irin yare na Duniya.
Malam Ya kara da cewa, Dan jarida mutum ne da ake daukarsa mai matukar ilimi da bin ka'ida, sabida haka zai zama abin tuhuma idan a samesa da aibu ko rashin cikakken Ilimi akan abinda yake rubutawa din.
A cikin jawabin nasa har ya bada misali da Sayyid Zakzaky (h), yake cewa, Akwai wata rana a wajan taron Mauludi sai Sayyid Zakzaky yazo yaga wani rubutu an rubuta kamar haka ‘Labbaika Ya Rusulullah’ take Malam ya nuna rashin Jin dadinsa da ganin rubutun domin akwai kuskure a ciki, sannan ya bukaci a sharesa a canja zuwa dai-dai. Kamata yayi rubutun ya kasance ‘Labbaika Ya Rasulallah’ maimakon ‘Labbaika Ya Rasulullah’.
Sabida haka yana dakyau ya kasance Dan Media ya kyautata rabutunsa kafin ya yada sa, ya gujewa kowane irin kuskure ta yadda zai karantu ya fitar da cikakkiyar ma'ana. Musamman mu da ake ganinmu ma'abota addini, to mu yafi kamata mu kasance ma'abota nizami da cika kowace ka'ida domin mune makwafin al’umma.
– Abbakar Ibraheem Kudan