Ƴan'uwantakar Addini: Abin haka yake Shinkafiyya Alkhairiyya; masu halin karamci.



MA'ASUMAH NIGERIA NEWS UPDATE

TARE DA SHANA ISLAM.


A farko Zan Fara da Sunan Allah Ubangijin Halittu Wanda ya sanya Annabi Muhammad (S) da iyalan gidansa tsarkaka sukafi kowa A Halittin nasa,, Ya Allah ka tsaren min Abun rubutuna a cikin dan wannan Rubutun da na baiwa Suna ABUN HAKA YAKE SHINKAFIYA AL'KAIRIYYA, wadda na fara da cewa, Zuwa na Shankafi ya Kara Tabbatar mun da cewa Lallai "Yan uwantaka na Addani ba Wasa bane, Akwai Soyayya da Yarda da Amana ga Kyautatawa ga sanin Darajjar Mutum ga Girmama matakin Mutum Kai gaskiya Dole ne na tsaya nayiwa Jagoran Harka Islamiyya Ta Nigeria Sheikh El'Zakzkay (H) godiya da jinjina.


Abba mun gode Bisa wannan Namijin kokarin da Kai wajen hada kawunan Bayin Allah ka Mai shesu "Yan uwanjuna masu Aminci da junan su da Nuna soyayya ga juna da taka tsantsan Dan gujewa Bacin ran wani a yayin Mu'amilat, wannan aikin sai Jagoran Gaskiya Allamah Sayyid Zakzaky (H) Allah yasawa su Abba da Alkairin'sa ilahee.


Ranar Juma'a 1/1/2021 muka baro inda muke domin zuwa Shinkafi ta Jihar Zamfara State, Motar mu ta fara tafiya ne Karfe 09:30 na safiyar Juma'a 1/1/2021 muka dauko Hanya a cewar Allah (S) tafiya Alhamdllh duk da yake munta tsaye tsaye da wasu "Yan Uzurorin da ba'a rasa ba, hakan yasa muka Bata lokaci akan hanya bamu samu isowa Gusau ba sai Misalin Karfe 05:00 pm,


Mun sauka Babbar tasha Gusau da misalin Karfe 05:40 pm inda mukayi yunkurin samun Mutar Da zata kaimu garin na Shankafi da ikon Allah Ta'alah yasa muka samu motar Amma ba Jama'a a cikin ta Saida muka jira Aka samu Jama'a sannan muka Kama hanyar Shankafi.


Alhamdllh a kan hanyar shin kafi bamu samu wata tangarta a tafiyar ba munyi tafiya cikin dadi ba tare da wata matsala ba inda Allah da iyawar sa sai gamu garin Shankafi misalin karfuna 09:20 da Something, muna sauka sai muka Kira Massa'ud Dan Masani Shankafi wadda ya kasance shne Wanda ya daukemu zuwa masauki Kuma mun Isa masauki lafiya misalin Karfe 09:40pm.


Bayan mun Isa get aka binciki kayan mu sannan aka bamu tamar shiga cikin Muhallin taro, wani abun sha awa da burgewa shine isar mu keda wuya a ciki Muka Kama karbar Kulawa da Kyautatawa ga Wakilan SHAFIN MA'ASUMAH,Nan muka zama abun ayiwa Hidama saboda "Yan uwantaka Haka Muka samu tarba ta musamman take aka rufemu da Abinci da Abunsha mukaci mukasha mukayi Sallam abun ganin Sha awa.


Wani Abunda ya Kara bani Shawa dajin Kara son kasan cewa a cikin Wakilan SHAFIN MA'ASUMAH shine ta yadda Naga Aminci da Yarda ga Mahalarta taron ba mai son wani ya cutu balle ya kasance wani ne zai cutar da wani, gaskiya wannan Amincin ya Birge ni saboda Aminci yasa kayan Hannun ka sai inda kaga damar ajeyawa bakada matsala batare da tunanin zaka rasa ba wani aiki sai Tarbiyar Jagoran Gaskiya Allamah Sayyid Zakzaky H).


Haka akaci gaba da Gudanar da Program cikin Tsari da Nizame Har zuwa ga Nasara, A Program din anyi Darussa a Fannoni maban banta daga Ilmomin Kimiya Na zamani da Sauran Darasoshin Dake Kara kusantar ga Bawa zuwa ga Allah (T) da tarbiyanstar da Ruhi akan Bautar Allah dayin komai domin Allah (T), Haka akace kaba da wayar da kawukan "Yan uwa akan Abunda ya Shafi Soshiyal Midiya.


Haka akaci gaba da Program har zuwa Ranar Rufe taron ba tare da wata matsala ba, Abun dai sai wadda ya gani Wanda bai samu Halarta wannan Muhimmin Taron ba gaskiya na tausaya mashi Dan anyi Mai Nisa sai dai muce sai yazo.


Muna Rokon Allah Ta alah ya maimaita muna ya sake hada Fuskokin mu da alkairin sa sannan ina amfani da wannan damar waje Rokon Afwn "Yan uwa akan Gazawata A'kan su Wanda nayiwa ba dai dai ba ya min Afwn Nima idan a kwai na yafe balantana ma banajin a kwai.


@Shana islam

5/1/2021.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post