Ana bikin duniya ake na Qiyama... Futa ta biyu (2)


 

A irin wannan lokacin, shine mafi zama dai_dai da mu anfani lokacin mu, don idan mukayi duba da yanayin rayuwa a da da kuma yanzu, zamuga banbanci ne karara, ci bayan da muka samu ya ninka cigaban yawa, kuma munada abubuwan da zasu cigaban tar damu, amma munki anfani da lokacin mu da kuma damar mu, domin mu cigabar da rayuwar mu, ta ahalinmu dama ta duniya baki daya.


Rashin yin abinda ya dace a lokacin daya dace, shine yake kara taka muhimmiyar rawa, wurin kara tabarbarewar rayuwarmu, ya zuwa yanzu ya kamata ace mun kai inda ba'a tunani a fannin cigaba, amma har yanzu ko indama ake tunanin bamu kaiba, bare mu wuce, shi al'amarin duniya ana yinsa ne ana neman lahira, akwai ababe da daman gaske da mukeyi anan, wa'yanda bazasu anfanemu anan dinba sai gobe kiyama.



Mu tashi mu kara zage dantse wajen gyara al'ummar mu da duniyar mu duka da lahira, nasara na samuwa ne daga lokacin da muka sakawa zukatanmu cewa zamu iya, kuma muka fara, samar da al'umma ta gari alhakine akan kowa, kayi kokari ka gyara kanka, yadda gyara wasu bazaya yi maka wahala ba, karka manta kanada ikon fada ne kawai, amma baka isa kayi dole a yi anfani da abinda ka fada ba,karmu manta da Allah a kowane al'amari namu, don shine mai komai saida izininsa komi ke tabbatuwa. Fatan kasancewarku cikin aminci da yardar ubangiji. 


Nagode


✍️ Zarah A Zamsarf

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post