- Muh'd Jawad Assaminaky
Yau ma ƴan uwa musulmi na Da'irar Saminaka da kewaye, sun fito domin nuna ƙin amincewa da ci gaba da riƙe jagoran harkar Musulunci a Nigeria; Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) da mai ɗakin sa Malma Zeenatuddeen.
Yan uwan sun fito ɗauke da hotunan kamar yadda suka saba fitowa tare da bayyana irin baƙin zalumcin da akeyi a ƙasar nan.
Malam Suleiman Rayyanu ne ya jagoranci gabatar da jawabi a muhallin. Al'umma da dama ne suka halarta. Muzaharar an danko ta daga Fudiyyah zuwa kasuwar ƴan Gwari dake garin na Saminaka.
Alhamdulillah an kammala lafiya cikin yar dan Allah.
#FreeSheikhZakzaky
- 2, Jan\2021. 19, J\Ula1442H.
Tags:
#FREE_ZAKZAKY