Sisters na Zainabiyyun reshen Sokoto sun gudanar da kayataccen Mauludi Sayyida Zainab (A.S) jiya Talata 5 ga wanat janairun 2021, a Hussainiyyar Imam Mahdi (AJTF) dake Unguwar Mabera a garin Sokoto.
An fara taron ne da budewa da Addu'a daga bakin Baba Bature. Sai karatun Al-Qura'ani mai girma, daga bakin Zainab Abdulmajid. An gabatar da Matasan JASAZ sukayi wakokin yabon Sayyida Zainab. Kammala are suke da wuya, aka yi taken (Anthem) Sahibul Asar.
Inda daga bisani Batula Birnin Kebbi ta karanto ziyarar Sayyida Zainab daga nesa. An dai gabatar da Suhaila Nura Tsafe domin yin takaitaccen jawabin makasudin taron.
Har wala yau anyi Display domin girmama Sayyida Zainab a wurin, wanda sisters na Zainabiyyun suka yi a wurin. Kammalawarsu ke da wuya aka gabatar da Fatima Dasuki Yawuri domin ta kanto Muqala Mai taken Gudummawar Mata a gwagwarmaya.
Malama Sa'adatu Usman itace tayi cikaken jawabin wacece Sayyida Zainab, inda Malama Shafa'atu Garkar Jibo ta gabatar da ita. Malama Sa'adatu ta kawo muhiman abubuwa sosai daga cikin rayuwar Sayyida Zainab, inda ta ce " sisters Babban abinda ya kamata mu kwafa daga rayuwar Sayyida Zainab shine saka cikaken hijabi. Domin Sayyida Zainab bata wasa da hijabi, haka ma Malama Zeenah matar Sheikh Zakzaky mun shaida cewa bata wasa da hijabi Don haka wajibin mune mu sisters mu rika saka cikaken hijabi. Domin Allah ne yayi Umurni da murika saka cikakken hijabi."
Bayan ta kammala jawabin ta aka mayar da abin magana zuwa ga Babban bako na musamman Sheikh Sidi Munir. Sheikh din ya tabo janubobi da daman Kuma masu matukar muhimmanci ga Maza da mata.
Bayan ya kammala jawabin sa, aka yanka alkaki (Cake) na nuna murna da ranar haihuwar Sayyida Zainab (A.S). Tare da raba walima ga sauran mahalarta taron.
Sannan jawabin godiya wanda Suhaila Abdullahi ta gabatar.
Daga karshe Sheikh Abba Bature ne ya rufe wannan taron da Addu'a.
Daga wakilinmu
Auwal M. Tukur
Tags:
Labaran Duniya